Wutar Lantarki Ta Samu Matsala, Mutane Za Su Shiga Duhu a Jihohi 4 a Najeriya
- Turken wutar lantarki da ke raba wuta zuwa jihohin Ribas, Kuros Riba, Bayelsa da Akwa Ibom ya samu matsala a daren Asabar
- Kamfanin TCN ya bayyana cewa tuni injiniyoyinsa suka fara aiki domin gano asalin matsalar da gyara ta cikin gaggawa
- TCN ya bai wa daukacin jama'ar yankin da wannan lamari ya shafa hakuri, ya na mai cewa ana gama gyara za a sako masu wuta babu bata lokaci
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Aba - Kamfanin Raba Wutar Lantarki na Najeriya (TCN) ya bayyana cewa babban turken wuta dake Aba/Itu ya samu matsala.
Kamfanin TCN ya ce wutar da ake rabawa ta kan turken mai karfin 132KV ta katse, lamarin da zai jefa wasu yankuna cikin duhu har zuwa lokacin da za a gyara.

Source: Getty Images
Hakan dai na kunshe ne a wata sanarwa da mai magana da yawun kamfanin TCN, Ndidi Mbah, ya fitar a ranar Lahadi, kamar yadda The Cable ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An dauke wuta a Akwa Ibom da jihohi 3
Sanarwar ta ce katsewar layin wutar ta faru ne sakamakon gocewar layin wuta wanda ya dakatar da wutar da ake bai wa Kamfanin Raba Wutar Lantarki na Fatakwal (PHED) da kuma na Jihar Akwa Ibom.
Kamfanin TCN ya bayyana cewa jihohin da PHED ke bai wa wutar lantarki sun haɗa da Bayelsa, Kuros Riba da Ribas.
Wace matsala aka samu a turken wutan?
A ruwayar jaridar Punch, sanarwar ta ce:
"Kamfanin TCN na sanar da al'umma cewa wuta ta dauke a turken lantarki na Aba/Itu a ranar Asabar, 13 ga Satumba, 2025, da misalin ƙarfe 1:03 na dare sakamakon tsallaken layin wuta."
“Hakan ya kawo cikas ga wutar lantarki da ake bai wa PHED tare da wutar da ake samarwa a Jihar Akwa Ibom.
"Ma’aikatanmu na sashen gyare-gyare sun riga sun fara aiki da gaggawa don gano matsalar da gyara ta domin dawo da wuta a yankunan da abin ya shafa.”
Kamfanin TCN ya bai wa jama’a hakuri bisa dauke wutar da aka yi sakamakon wannan matsala da ta faru tare da tabbatar da cewa za a dawo da wuta da zarar an kammala gyara.

Source: UGC
Yadda TCN ke fama da lalacewar wuta
TCN ya kuma tunatar da cewa a ranar 8 ga Satumba, an samu guguwa da hadari da ta yanke layin wutar 132KV Otukpo–Nsukka–New Haven, wanda ya haddasa gobara.
Sanarwar ta ce wannan lamarin ya yi sanadiyyar ƙonewar wani gida da aka gina ƙarƙashin layin wutar, ya ƙone wata mota da aka ajiye a wurin, tare da halaka shanu guda biyu da suka faɗa a layin.
Za a daina dauke wutar lantarki a Najeriya
A wani labarin, kun ji cewa Gwamnatin Tarayya ta yi ikirarin cewa nan ba da jimawa ba yan Najeriya za su ga an daina dauke wutar lantarki kwata-kwata.
Ministan Makamashi, Adebayo Adelabu ya ce ƙoƙarin da Gwamnatin Tarayya ke yi ya fara haifar da sakamako mai kyau domin wutar Lantarki da ake samarwa yanzu ta.zarce ta baya.
Ya ce gwamnati na samar da hasken wutar lantarki a jami’o’i, asibitocin koyarwa, cibiyoyin kiwon lafiya, hukumomin gwamnati da garuruwa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

