Ambaliyar Ruwa Ta Lalata Gidaje da Gonaki a Kebbi, Gwamnati Ta Ba da Tallafi

Ambaliyar Ruwa Ta Lalata Gidaje da Gonaki a Kebbi, Gwamnati Ta Ba da Tallafi

  • An samu aukuwar ambaliyar ruwa wadda ta lalata gidaje da gonaki masu yawa a jihar Kebbi da ke yankin Arewa maso Yammacin Najeriya
  • Ambaliyar ruwan dai ta shafi wasu kauyuka ne a kananan hukumomin Dandi da Suru na jihar Kebbi
  • Gwamnatin jihar ta kai ziyarar jaje inda ta ba tallafin kudi da abinci ga mutanem da ambaliyar ruwan ta shafa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kebbi - Ambaliyar ruwa mai tsanani ta lalata manyan gadoji biyu, gidaje da gonaki da dama a kananan hukumomin Dandi da Suru na jihar Kebbi.

Ambaliyar, wadda ta auku a ranar Alhamis, ta ruguza gadoji guda biyu, ɗaya a garin Fana da kuma wata gadar da ke haɗa hanyar Dakingari-Kyangakwai.

An samu ambaliyar ruwa a Kebbi
Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris, lokacin ganawa da manema labarai Hoto: @NasirIdrisKIG
Asali: Facebook

Tashar Channels tv ta rahoto cewa gidaje da gonaki da dama sun nutse a cikin ruwa a yankunan da abin ya shafa.

Kara karanta wannan

Bayan fitowa daga komar EFCC, Tambuwal ya sha alwashi kan gwamnatin APC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnatin Kebbi ta kai ziyarar jaje kan ambaliyar ruwa

Mataimakin Gwamnan jihar Kebbi, Sanata Umar Tafida, ya mika ta’aziyyar gwamnati ga waɗanda abin ya shafa a kauyukan Fana, Aljannare da Kampani da ke cikin kananan hukumomin Dandi, Suru da Argungu.

Haka kuma, ya gabatar da kayan tallafi da taimakon kuɗi na Naira miliyan 70 domin rage wa jama’a wahalhalu.

A yayin ziyarar jaje zuwa yankunan da ambaliyar ruwan ta shafa a ranar Asabar, mataimakin gwamnan ya tabbatar wa mazauna yankin cewa gwamnati za ta ci gaba da tallafa musu tare da sanar da shirin gina sababbin gadojin da suka rushe.

Ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta bayar da tallafin N50m tare da buhunan shinkafa 600 ga waɗanda abin ya shafa a Fana, Maigwaza, da Tungar Beddi a karamar hukumar Dandi.

Haka kuma ta ba da N10m da buhunan shinkafa 250 ga kauyen Aljannare a karamar hukumar Suru, sannan kuma ta ba da N10m da buhunan shinkafa 250 ga waɗanda abin ya shafa a kauyen Kampani na karamar hukumar Argungu.

Kara karanta wannan

El Rufai: Gwamnatin Kaduna ta karyata zargin ADC ana shirin zaben cike gurbi

Sanata Umar Tafida ya yi addu’ar Allah ya aukuwar rin wannan ibtila’i a nan gaba, tare da yin kira ga jama’a da su karɓi wannan masifa a matsayin kaddarar Ubangiji.

An samu aukuwar ambaliyar ruwa a Kebbi
Taswirar jihar Kebbi, Najeriya Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Gwamnatin Kebbi ta samu yabo

A jawabinsu daban-daban, shugaban karamar hukumar Dandi, Mansur Isah, da ɗan majalisar da ke wakiltar mazabar Dandi, Sulaiman Abubakar, sun nuna godiya ga gwamnatin jihar bisa gaggawar da ta yi wajen kawo agaji.

Mansur Isah ya shaida wa mataimakin gwamnan cewa mutum guda ya rasu a wannan ibtila’in, yayin da gidaje da dama suka rushe, kuma daruruwan gonaki suka nutse.

Ambaliyar ruwa ta yi barna a Kebbi da Neja

A wani labarin kuma, kun ji cewa an samu aukuwar mummunar ambaliyar ruwa a jihohin Kebbi da Neja da ke Arewacin Najeriya.

Ambaliyar ruwan ta lalala amfanin gonakin mutane masu yawa a karamar hukumar Argungu ta jihar Kebbi.

Mahukunta sun yi kira ga jama'a da su ci gaba da yin taka tsan-tsan domin gujewa aukuwar irin hakan a gaba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng