Jerin Manya da 'Yan Siyasar da Suka Yi Magana kan Lafiyar Shugaba Tinubu

Jerin Manya da 'Yan Siyasar da Suka Yi Magana kan Lafiyar Shugaba Tinubu

Abuja - Batun lafiyar shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ne babban abin da aka fi tattaunawa a kai a Najeriya a yan kwanakin nan.

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Mutane, musamman a kafafen sada zumunta sun rika yada labarin cewa Shugaba Tinubu ba shi da lafiya, kuma hakan ne ya sa aka daina ganinsa a bainar jama'a.

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.
Fadar shugaban kasa ya karyata labarin cewa Tinubu ba shi da lafiya Hoto: @OfficialABAT
Asali: Twitter

Yadda aka fara yada labarin lafiyar Tinubu

Jita-jitar ta samo asali ne daga wani rahoto da cibiyar ICIR ta wallafa, wanda ya ambato wasu majiyoyi na cewa Tinubu ba shi da lafiya har an fara shirin fitar da shi kasar waje.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton ya yi ikirarin cewa rashin lafiyar da Shugaba Tinubu ke fama da ita ce ta sanya aka daina ganinsa a wuraren taruka da ya kamata ya halarta.

Kara karanta wannan

Ana batun rashin lafiyar Tinubu, Gwamna Radda zai tafi jinya domin duba lafiyarsa

A cewar majiyoyin da cibiyar ta tattara, mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ne ke wakiltarsa, lamarin da ya kara jefa shakku a zukatan yan Najeriya.

Manyan da suka yi magana kan lafiyar Tinubu

Tun bayan bullar wannan labari, fadar shugaban kasa, manya da yan siyasa da dama sun fito sun karyata, wasu ma sun samu ganawa da Tinubu a Aso Rock.

A wannan rahoton, Legit Hausa ta tattaro maku duk wadanda suka yi magana kan lafiyar Shugaba Tinubu da kuma abin da suka ce, ga su kamar haka:

1. Kakakin shugaban kasa, Bayo Onanuga

Mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga ya karyata rahoton rashin lafiyar mai girma Tinubu.

Onanuga ya shaidawa cibiyar ICIR cewa Tinubu na cikin koshin lafiya kuma yana gudanar da aikinsa sabanin labarin karya da aka ba su.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga.
Fadar shugaban kasa ta musanta rade-radin rashin lafiyar Bola Tinubu Hoto: @aonanuga1956
Asali: Twitter

Yayin da Daily Trust ta tuntube shi don jin gaskiyar labarin, kakakin shugaban kasar ya bukaci a yi watsi da jitar-jitar wacce ya bayyana da mara tushe.

Kara karanta wannan

"Ina da tabbaci," Bwala ya hango yadda za ta kaya tsakanin Jonathan da Tinubu a 2027

Da aka tambaye shi kan dalilin rashin fitowar Tinubu bainar jama'a, Bayo Onanuga ya amsa da cewa shugaban na da yancin gudanar da ayyuka daga gida.

"Ba abin da ke damun shugaban kasa, yana cikin koshin lafiya, doka ta ba shi yancin yin aiki daga gida ko wani wuri da ya ga dama, ina tabbatar maku da cewa lafiyarsa kalau," in ji shi.

2. Sanata Orji Uzor Kalu

Sanata mai wakiltar mazabar Abia ta Arewa a majalisar dattawa, Orji Uzor Kalu ya musanta labarin da ake yadawa game da rashin lafiyar Shugaba Tinubu.

Kalu, tsohon gwamnan Abia ya ce ya yi magana da shugaban kasa a wayar salula a daren ranar Litinin 11 ga watan Agustan 2025.

Ya tabbatar wa yan Najeriya cewa Tinubu na cikin koshin lafiya, yana mai cewa gajiya ce kawai wacce kowa na iya jin kasala har ya gaza fita wurin aiki.

Sanata Orji Kalu da Shugaba Bola Tinubu.
Sanatan Abia, Orji Uzor Kalu ya yi waya da Shugaba Bola Ahmed Tinubu Hoto: Senator Orji Uzor Kalu
Asali: Facebook

A wani faifan bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Sanata Kalu ya ce:

Kara karanta wannan

Ana jita jitar rashin lafiya, Tinubu ya yi magana, ya fadi gwamnonin da zai yi alaƙa da su

"Na yi magana da shi (Shugaba Tinubu) awanni biyu da suka wuce kuma yana cikin koshin lafiya, gajiya ce kawai yanzu yana shirye-shiryen zuwa Japan, sannan zai tsaya a Brazil."

3. Hadimin shugaban kasa, Abdul'aziz Abdul'aziz

Mai ba shugaban kasa shawara ta musamman kan harkokin jaridu, Abdulaziz Abdulaziz ya ce gaba daya rahotannin rashin lafiyar Tinubu ba gaskiya ba ne.

Ya ce jita-jitar da ake yadawa abin dariya ce duba da yadda ake yada labarin da yake karya mara tushe balle makama.

Abdulaziz Abdulaziz tare da maigidansa Shugaba Tinubu.
Hadimin shugaban kasa, Abdulaziz Abdulaziz ya tabbatar da lafiyar mai girma Tinubu Hoto: Abdulaziz Abdulaziz
Asali: Facebook
"Dariya abin yake ba mu domin mun san abin da ake yadawa karya ce. Shugaban kasa mutum ne dan adam kamar kowa, kamar ni da kai, zai iya yin rashin lafiya, amma a yanzu dai lafiyarsa kalau," in ji shi.

Hadimin shugaban kasar, Abdul'aziz ya yi wannan bayani ne yayin wata tattaunawa da DCL Hausa kan batun lafiyar Bola Tinubu.

4. Jagora a APC, Farouk Adamu Aliyu

Kara karanta wannan

Magana ta kare, bidiyon Shugaba Tinubu ya bayyana ana tsaka da jita jitar ba shi da lafiya

Tsohon dan majalisar wakilai kuma jigo a APC, Farouk Adamu Aliyu ya bayyana cewa ya samu ganin Shugaba Tinubu kuma babu wata alamar da ke nuna ba shi da lafiya.

A cewarsa, ya shafe kusan mintuna 30 suna tattaunawa da shugaban kasa, amma bai ga wani sauyi daga yadda ya saba ganinsa ba.

Farouk Adamu Aliyu tare da Tinubu a Aso Rock.
Hon. Farouk Adamu Aliyu ya hadu da Tinubu a lokacin da akw rade-radin ba shi da lafiya Hoto: @ImranMuhd
Asali: Twitter

A wata hira da DCL Hausa, jigon ya ce cuta tana iya hawa kan kowa, amma dai Shugaba Tinubu lafiyarsa kalau.

Farouk Aliyu ya ce:

"Na farko dai cuta tana kan kowa, amma a yadda na gan shi, babu alamar ciwo sai dai dattijantaka wanda idan shekaru suka cimma mutum zai samu irin wannan.
"A cikin maganganun da muka yi, ya gaya mani cewa zai yi tafiya zuwa wata kasa, daga nan ya wuce wata kasa, ka ga mutum mara lafiya zai yi irin wannan tafiye-tafiye?"

5, Gwamna Soludo na jihar Anambra

Kara karanta wannan

Bayan yada jita jitar mutuwar Tinubu a daren jiya, hadiminsa ya fadi gaskiya

Gwamnan jihar Anambra, Charles Chikwuma Soludo, na daya daga cikin manyan mutanen da suka ziyarci Shugaba Bola Ahmed Tinubu yayin da ake rade-radin ba shi da lafiya.

A rahoton da The Cable ta kawo, gwamnan ya bayyana cewa Shugaba Tinubu na cikin koshin lafiya sabanin yadda mutane ke yadawa.

Shugaba Tinubu da Gwamna Soludo a fadar shugaban kasa.
Gwamnan Anambra ya hadu da mai girma shugaban kasa a Aso Rock Hoto: @ImranMuhdZ
Asali: Twitter

Da yake hira da manema labarai a fadar shugaban kasa bayan ganawa da Tinubu a ofishinsa, Soludo ya ce:

"Shugaba Tinubu yana cikin farin ciki, yana cikin ƙoshin lafiya, yana karɓar baƙi da sauran aikace-aikace."

Shugaba Tinubu zai yi tafiya zuwa kasashe 2

A wani labarin, kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu zai bar Najeria zuwa wasu kasashe biyu domin halartar taruka a ranar Alhamis, 14 ga watan Agusta, 2025.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya ce Tinubu zai tafi Japan da Brazil domin halartar taruka da ganawa da shugabanni.

Ana sa ran ministoci da wasu manyan jami'an gwamnatin Najeriya za su raka shugaban kasar zuwa kasashen guda biyu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

iiq_pixel