An Yi Rashi a Najeriya, Babban Sarki Ya Yi Bankwana da Duniya Yana da Shekaru 82

An Yi Rashi a Najeriya, Babban Sarki Ya Yi Bankwana da Duniya Yana da Shekaru 82

  • An tabbatar da rasuwar fitaccen basarake a Najeriya yana da shekaru 82 bayan fama da jinya na wani lokaci
  • Alara na Aramoko Ekiti, Oba Olu Adegoke Adeyemi, ya rasu bayan ya yi shugabanci mai cike da hikima da nasarori
  • Iyalansa sun bayyana mulkinsa a matsayin lokaci da ya kawo hadin kai, ci gaban al’adu, zaman lafiya da inganta rayuwar matasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Jihar Ekiti - Rahotanni sun tabbatar da rasuwar fitaccen basarake a jihar Ekiti da ke Kudu maso Yamma a Najeriya

An ce Sarkin na Aramoko Ekiti, Oba Olu Adegoke Adeyemi, ya koma ga mahaliccinsa yana da shekara 82 a duniya.

Babban Sarki ya rasu a Najeriya
An sanar da rashin fitaccen Sarki a jihar Ekiti. Hoto: Oba Olu Adegoke Adeyemi.
Asali: Twitter

An sanar da rasuwar babban Sarki a Ekiti

Rahoton The Nation ya ce Alara ya mutu a ranar Juma’a 8 ga watan Agustan 2025 bayan ya yi fama da jinya.

Kara karanta wannan

Biki bidiri: An daura wa jaruma Rahama Sadau aure a jihar Kaduna

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majiyoyi suka ce marigayin ya shahara saboda shugabanci mai nagarta, hikima, da jajircewa wajen inganta walwalar al’ummarsa.

Wata sanarwa daga iyalansa a ranar Asabar ta bayyana mulkinsa a matsayin lokaci na hadin kai, kare al’adu, da ci gaba mai dorewa.

An yabawa salon shugabancin marigayi Sarki

Iyalansa sun ce, shugabancinsa ya sha bamban da shirin sasanta rikice-rikice, karfafa matasa, da gina ababen more rayuwa da suka karfafa zumunci.

Sanarwar ta ce:

“Tasirin Oba Adeyemi ga al’umma zai ci gaba da kasancewa abin tunawa a matsayin shaida ta abin alheri da ya yi na dindindin."
An sanar da rasuwar babban Sarki a Ekiti
Al'umma sun shiga damuwa bayan sanar da mutuwar babban Sarki. Hoto: Legit.
Asali: Original

Yaushe za a yi jana'izar marigayi Sarki?

A cewar iyalan, za a sanar da jadawalin jana’iza daga baya domin karrama basaraken da ya sadaukar da rayuwarsa wanda mutane ke yabonsa saboda shi masoyan jama'a ne.

An haife shi a ranar 4 ga Disamba, 1942, rayuwarsa ta kasance mai cike da hidima a fannoni da dama, Sahara Reporters ta tabbatar.

Kara karanta wannan

Davido: Mawakin Najeriya ya yi auren kece raini, ya kashe sama da Naira biliyan 5

Ya fara aiki a matsayin malami, daga baya ya zama babban jami’in gwamnati, sannan ya shugabanci tsohuwar karamar hukumar Ifesowapo.

Ana jimamin mutuwar Sarki da ake kauna

Kaunarsa ga cigaban al’umma ta ci gaba bayan hawan karagar mulki a 2009 wanda al'umma da dama ke nuna alhini kan rashin da aka yi.

A lokacin da yake babban shugaban Jami’ar Jihar Ekiti, marigayi Oba ya jagoranci ayyuka na inganta ilimi da fadada damar shiga ga daliban yankin.

Al'ummar yankin da dama sun shiga wani irin yanayi bayan mutuwar Sarki yayin da ake yabonsa kan kokarin da ya yi.

An kaure tsakanin addinai kan birne Sarki

Mun ba ku labarin cewa Kungiyar Limamai da Alarammomi ta Ogun ta nuna damuwa kan hana zirga-zirga da ake shirin kakabawa a Ikolaje da Idiroko saboda jana’izar sarki.

Limaman sun ce wannan matakin ya saba wa kundin tsarin mulki da kuma hukuncin kotu da yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma tun 2017.

Sun bukaci Gwamna Dapo Abiodun ya sa baki don hana wannan abu, da kare rayuka da dukiyoyin jama’a daga barazanar rikici da tashe-tashen hankali.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.