'Yan Sanda Sun Saki Sowore, Ya Yi Zazzafar Magana bayan Shakar 'Yanci
- Rahotanni na nuni da cewa an saki Omoyele Sowore daga tsarewar da ya ce ba ta da dalili kuma ba bisa doka aka yi ta ba
- Ya bayyana cewa ‘yan sanda sun karya masa hannu tun lokacin da aka kama shi, kuma ba a kawo masa likita ba
- Sowore ya ce wannan ba lokacin murna ba ne, amma ya gode wa ‘yan Najeriya da suka hada kai suka nemi a sake shi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - An saki ɗan gwagwarmayar kare haƙƙin ɗan Adam, Omoyele Sowore, daga tsarewar da 'yan sanda suka yi masa a Abuja.
Sowore ya bayyana cewa tsarewar ba ta da wani tushe na doka, kuma an kama shi ne saboda ra’ayinsa na adawa da gwamnatin Najeriya.

Asali: Facebook
'Dan gwagwarmayar ya wallafa sakon cewa ya shaki 'yanci ne a shafinsa na X da yammacin yau Juma'a.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“An mani illa a hannu,' Omoyele Sowore
Sowore ya bayyana cewa tun bayan kama shi aka tsare shi a hedikwatar ‘yan sanda da ke Abuja ba a kula da lafiyarsa ba.
A wata hira da aka yi da shi kafin a sake shi, ya bayyana cewa:
“Ina da rauni a hannuna, sun ɗaure min da bandeji, amma tun jiya ba a kawo likita ba, sai jiya suka kawo jami'in lafiya, ba likita ba,”
Ya kara da cewa an kawo ‘yan jarida domin a nuna kamar yana cikin koshin lafiya ne, duk da cewa hakikanin gaskiya ba haka ba ne.

Asali: Twitter
Maganar Yele Sowore bayan ya fito
Bayan sako shi daga tsarewar, Sowore ya yi godiya ga 'yan Najeriya da suka tsaya masa bayan kama shi.
Sowore ya wallafa cewa:
“An sake ni daga wannan tsarewar da ba ta da adalci. Amma wannan ba wani abin murna ba ne. Ina matuƙar godiya a gare ku, saboda ba ku yi kasa a gwiwa ba.”
Ya ce abin da ya faru ya sake bayyana karfin haɗin kan al’umma da yadda ‘yan Najeriya ke iya tunkarar zalunci idan sun tashi tsaye.
An yi zanga-zanga a jihohi da dama
Punch ta wallafa cewa tuni masu goyon bayan Sowore suka gudanar da zanga-zanga a jihohi da dama ciki har da Legas, Abuja, Oyo da Osun, inda suka bukaci a sake shi nan take.
A lokacin da ya ke magana daga tsarewa ranar Juma’a, Sowore ya ce:
“Babu wani dalili da ya sa za a kama ni. Babu wata doka da ta ba IGP damar kama ‘yan Najeriya saboda kawai yana jin ra’ayinsu na adawa barazana ne gare shi.”
Sowore ya yi zanga zangar 'yan sanda
A wani rahoton, kun ji cewa Omoyele Sowore da wasu 'yan gwagwarmaya sun yi zanga zangar 'yan sanda a Abuja.
Omoyele Sowore ya bayyana cewa sun yi zanga zangar ne domin kwatowa 'yan sanda hakkinsu bayan kammala aiki.
Sun gudanar da zanga zangar ne a hedikwatar 'yan sanda da ke birnin tarayya Abuja, kuma ta samu halartar mutane da dama.
Asali: Legit.ng