Yadda Peter Obi Ya Kai Zuciya Nesa, Ya Ki Karbar Kyautar N120m
- Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar LP, Peter Obi ya bayyana wani hali da yake da shi na ƙin abin duniya
- Peter Obi ya bayyana yadda ya ƙi karɓar kyautar N120m da aka yi masa lokacin da yake a matsayin gwamna
- Ya bayyana cewa lokacin da aka yi masa kyautar ya buƙaci a kai kuɗaɗen zuwa inda aka fi buƙatarsu
FCT, Abuja - Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar LP a zaɓen 2023, Peter Obi, ya bayyana yadda ya ƙi karɓar kyautar N120m.
Peter Obi ya ce ya ƙi karɓar kyautar gida mai darajar N120m da aka shirya ba shi a bikin zagayowar ranar haihuwarsa ta shekaru 50 a lokacin da yake gwamnan jihar Anambra.

Source: UGC
Peter Obi ya bayyana hakan ne a cikin wani rubutu da ya sanya a shafinsa na X.
Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasan ya ce maimakon karɓar kyautar, sai ya roƙi a yi amfani da kuɗin wajen gina ajujuwa.
Peter Obi wanda ya cika shekaru 64 a ranar Asabar, 19 ga watan Yulin 2025 ya samu saƙonnin taya murna daga ƴan Najeriya.
A cikin rubutun na sa tsohon gwamnan Anambra ya gode wa dukkan waɗanda suka taya shi murnar zagayowar ranar haihuwarsa ta shekaru 64 a duniya.
Yadda Peter Obi ya ƙi karɓar N120m
Ya bayyana cewa ko da yake ba ya shirya bukukuwan ranar haihuwarsa kai tsaye, ya fi so a karkatar da duk wata gudunmawa da za a ba shi zuwa ayyukan da za su amfani jama’a.
"Ina tuna lokacin da na cika shekaru 50 a lokacin ina gwamna, wata cibiya ta nemi ta gina min gida a ƙauyena. Lokacin da na tambaya kuɗin da za a kashe, sai suka ce N120m."
"Sai na nemi a mayar da kuɗin don gina ajujuwa a makarantu guda uku da ke Agulu, Ekwulobia da Abatete. Sai suka amince kuma tasirin hakan ya yi amfani sosai."

Kara karanta wannan
Gaskiya ta fito: Tsohon gwamnan PDP ya fadi dalilin yin aiki don kayar da Atiku a 2023
- Peter Obi
Peter Obi ya sha tsallake kyaututtuka
Peter Obi ya kuma bayyana cewa wata ƙungiya ta shirya masa liyafa a ranar haihuwarsa da kuɗi N20m, amma ya ƙi yarda inda ya buƙaci su saka kuɗin a harkar ilmi.

Source: Twitter
Ya ce daga ƙarshe ƙungiyar ta bai wa makarantu kwamfutoci 200 domin rabawa a faɗin jihar Anambra.
Obi ya ce ya yi amfani da damar zagayowar ranar haihuwarsa wajen yi wa Najeriya addu’a a birnin Rome, inda ya yi kira ga shugabannin ƙasa da su sauya halayensu.
Dalilin Peter Obi, El-Rufai na ƙin shiga ADC
A wani labarin kuma, kun ji jam'iyyar ADC ta bayyana dalilin da ya sa har yanzu Peter Obi da Nasir El-Rufai ba su zama mambobinta ba.
Sakataren jam'iyyar na ƙasa, Mallam Bolaji Abdullahi, ya bayyana cewa ƴan siyasan suna da wasu abubuwa da suke son kammalawa a jam'iyyunsu.
Mallam Bolaji Abdullahi ya bayyana cewa da zarar sun kammala, za a yi musu rajista a matsayin mambobin jam'iyyar ADC.
Asali: Legit.ng

