An Tafi da Gawar Buhari zuwa Mahaifarsa Daura bayan Ta Iso Najeriya

An Tafi da Gawar Buhari zuwa Mahaifarsa Daura bayan Ta Iso Najeriya

  • Gawar marigayi tsohon shugaban ƙasan Najeriya, Muhammadu Buhari ta iso Najeriya daga birnin Landan na Birtaniya
  • Shugaba Tinubu ya karɓi gawar magabacin nasa wanda ya rasu a ranar Lahadi, 15 ga watan Yulin 2025
  • Bayan isowar gawar, an wuce da ita zuwa mahaifarsa ta Daura inda za a yi masa jana'iza tare da binne shi bisa tsarin addinin Musulunci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Katsina - Gawar marigayi tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari na kan hanyar zuwa garinsa na haihuwa, Daura.

An tafi da gawar Muhammadu Buhari ne don gudanar da jana’iza da kuma birne shi da rana a ranar Talata, 15 ga watan Yulin 2025.

An wuce da gawar Buhari zuwa Daura
An tafi da gawar Muhammadu Buhari zuwa Daura Hoto: @Imranmuhdz
Source: Twitter

Jaridar Leadership ta ce an tafi da gawar marigayin ne ta hanyar mota zuwa Daura, a arewacin jihar Katsina.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gawar Muhammadu Buhari ta tafi Daura

Kara karanta wannan

Bidiyo: Iyalai na hawaye, Shugaba Tinubu ya karɓi gawar Muhammadu Buhari a Katsina

An tafi da gawar ne bayan girmamawa ta soja a filin jirgin sama na Umaru Musa Yar’Adua da ke Katsina, domin karrama Buhari.

An saukar da gawar marigayin a filin jirgin sama na Umaru Musa Yar’Adua da misalin ƙarfe 2:00 na rana a ranar Talata.

Gawar Buhari ta iso ne daga birnin Landan, inda ya rasu a ranar Lahadi, 13 ga watan Yuli, yana da shekara 82, bayan gajeruwar rashin lafiya.

Rasuwar marigayin ta saka ƴan Najeriya da dama cikin jimami da kaɗuwa bisa babban rashin da aka yi.

An karɓi akwatin da ke ɗauke da gawarsa cikin nutsuwa da cikakkiyar girmamawar soja, inda manyan jami’an gwamnati, iyalansa, da manyan baƙi suka taru a filin jirgin domin girmamawa na ƙarshe.

Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ne ya jagoranci tawagar gwamnatin tarayya daga Birtaniya zuwa gida, kamar yadda Shugaba Bola Tinubu ya umarta.

Shugaba Tinubu ya je Katsina

Shugaba Tinubu da kansa ya isa Katsina tun da farko domin karɓar gawar tsohon shugaban ƙasan na Najeriya.

Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umar Radda, tare da wasu manyan jami’an gwamnati ne suka tarbe shi a filin jirgin sama.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Yadda aka fito da gawar Buhari daga jirgi da manyan mutanen da aka gani

An tafi da gawar Buhari zuwa Daura
An wuce da gawar Buhari zuwa Daura Hoto: @MSIngawa
Source: Twitter

Uwargidan shugaban ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, tana Katsina domin halartar jana’izar marigayin.

Buhari wanda ya riƙe matsayin shugaban ƙasa na soja daga 1983 zuwa 1985, sannan ya sake shugabantar Najeriya a matsayin farar hula daga 2015 zuwa 2023, za a birne shi a Daura bisa tsarin addinin Musulunci.

Tarin jama’a, ciki har da shugabannin siyasa, sarakunan gargajiya, baki daga ƙasashen waje, da al’ummar gari, za su halarci jana’izar domin girmama Buhari wanda da dama daga cikin ƴan Najeriya ke kira “Mai Gaskiya".

Shugaba Tinubu ya karɓi gawar Buhari

A wani labarin kuma, kun ji cewa mai girma shugaban ƙasa Bola Tinubu ya karɓi gawar wanda ya gabace shi a shugabancin Najeriya, Muhammadu Buhari.

Mai girma Bola Tinubu ya karɓi gawar ne a jihar Katsina daga hannun tawagar gwamnatin Najeriya ƙarƙashin jagorancin mataimakin shugaban ƙasa, Ƙashim Shettima.

Kashim Shettima tare da wasu daga cikin iyalan marigayi tsohon shugaban ƙasan ne suka yi wa gawar rakiya daga birnin Landan na ƙasar Birtaniya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng