Garba Shehu Ya Fadi Halin da Buhari Yake ciki bayan Kwantar da Shi a Asibiti
- Garba Shehu ya tabbatar da cewa an duba lafiyar tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a ƙasar Birtaniya (UK).
- Tsohon mai magana da yawun shugaban ƙasan ya kwantar wa ƴan Najeriya hankali, inda ya yi addu’ar samun cikakken sauƙi ga Buhari
- Buhari dai na da tarihin zuwa Birtaniya don neman lafiya akai-akai, ciki har da dogon zaman da ya yi a shekarar 2017
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - A daren ranar Juma’a, 11 ga watan Yuli, Garba Shehu, mai magana da yawun tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya yi magan a kan rashin lafiyarsa.
Garba Shehu ya bayyana cewa rashin lafiyar tsohon shugaban ƙasa mai shekaru 82 ba ta yi tsanani ba kamar yadda aka ruwaito.

Source: Twitter
Garba Shehu, wanda ya kasance babban mataimaki na musamman kan harkokin yada labarai a lokacin gwamnatin Buhari, ya bayyana hakan ne a shirin 'Politics Today' na Channels Tv.

Kara karanta wannan
Abin ɓoye ya fito fili: An faɗi dalilin rufa rufa kan rashin lafiyar Buhari a mulkinsa
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon shugaban ƙasan ya jima yana fama da rashin lafiya, amma ana ganin yana samun sauƙi a halin yanzu.
Tinubu ya tura Shettima duba Buhari
Shugaba Bola Tinubu ya tura mataimakinsa, Kashim Shettima, don ziyartar Buhari a wani asibiti da ke birnin Landan a ranar Litinin, 7 ga watan Yuli, kamar yadda wasu majiyoyi masu tushe suka bayyana wa ƴan jarida.
Shettima dai ya kasance a birnin Addis Ababa, ƙasar Habasha, bisa gayyatar Firamiinista Abiy Ahmed Ali, domin halartar ƙaddamar da Green Legacy Initiative (GLI) na ƙasar ta Gabashin Afirka.
Sai dai daga can, Shugaba Tinubu wanda a lokacin yake wata ziyarar aiki a ƙasar St. Lucia, ya umurci Shettima da ya wuce zuwa Landan domin duba lafiyar tsohon shugaban ƙasan.
A cewar jaridar The Cable, Shugaba Tinubu ya umarci Shettima da ya tantance halin da Buhari ke ciki, tare da tabbatar da cewa ya samu cikakken goyon baya don murmurewa gaba ɗaya.
Shettima ya tashi daga Addis Ababa a daren Lahadi, 6 ga Yuli, sannan ya isa birnin Landan a ranar Litinin, 7 ga Yuli, inda ya wuce zuwa wani asibiti da ba a bayyana ba domin isar da saƙon Shugaba Tinubu ga Buhari.

Source: Twitter
Me Garba Shehu ya ce kan lafiyar Buhari?
Tsohon hadimin shugaban ƙasan ya bayyana cewa an sallami Buhari daga asibiti.
"An sallami Buhari. Rashin lafiyar bai kai yadda aka ruwaito ba... yana cikin yanayin murmurewa ne. Kullum yana samun sauƙi har ya warke gaba ɗaya."
- Garba Shehu
Buhari dai ya sauka daga mulki a shekarar 2023, inda ya koma rayuwa cikin natsuwa a garinsu na Daura da ke jihar Katsina.
Zaman da ya ɗauka a waje har yanzu na janyo tambayoyi kan lafiyarsa da kuma yiwuwar dawowarsa Najeriya nan kusa.
Jonathan ya zargi Buhari
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban ƙasan Najeriya, Goodluck Jonathan, ya yi zargi kan Muhammadu Buhari.
Goodluck Jonathan ya zargi gwamnatin tsohon shugaban ƙasan da gallazawa jami'an gwamnatinsa kan badaƙalar Malabu.
Tsohon shugaban ƙasan ya ce gwamnatin Buhari ta riƙa yin abin da mutane suka kwatanta da farautar jami'an gwamnatinsa.
Asali: Legit.ng
