Tinubu Ya Roki Alfarma wajen 'Yan Najeriya, Ya Fadi Abin da Yake So a Yi Masa

Tinubu Ya Roki Alfarma wajen 'Yan Najeriya, Ya Fadi Abin da Yake So a Yi Masa

  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci ƴan Najeriya da su ƙara haƙuri kan wanda suke yi a yanzu
  • Mai girma Bola Tinibu ya bayyana cewa bai manta ba da irin tsammanin da ƴan Najeriya suke yi kan gwamnatinsa ba
  • Shugaba Tinubu ya nuna cewa abubuwa sun fara sassaita a ƙasar nan kuma matakan da ya ɗauka za su haifar da ɗa mai ido a nan gaba

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya miƙa ƙoƙon bararsa ga ƴan Najeriya da yake jagoranta.

Shugaba Tinubu ya roƙi ƴan Najeriya da su ƙara yin haƙuri da shi.

Shugaba Bola Tinubu
Tinubu ya bukaci a kara hakuri da shi Hoto: Ibrahima Kaulaha Mohammed
Source: Twitter

Jaridar The Punch ta ce Shugaba Tinubu ya bayyana hakan ne yayin ƙaddamar da sashe na farko mai tsawon kilomita 30, na aikin titin gaɓar teku na Legas zuwa Calabar mai tsawon kilomita 750, a ranar Asabar.

Kara karanta wannan

"Sun cika mantuwa": Hadimin Tinubu ya caccaki masu sukar shugaban kasa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya buƙaci ƴan Najeriya su ƙara haƙuri

Mai girma Bola Tinubu ya bayyana cewa yana sane da irin tsammanin da ƴan Najeriya suke yi a kansa.

"Na san a wannan matakin, tsammaninku yana da yawa, kuma mutane na fama da ƙalubale masu tsanani."
"Ina amfani da wannan dama na roƙi ƴan Najeriya da su yi haƙuri, akwai fata, kuma wannan fata zai tabbata."
"Za ku yi alfahari da ribar da za ku samu. Daga ƙarshe akwai alamun nasara. Farashin kaya na raguwa, mun kawar da cin hanci da rashawa a kasuwancin canjin kuɗi, mun rage cin hanci a tallafin man fetur zuwa mafi ƙanƙanta."
"Wannan duk domin ku ne ƴan ƙasa. Muna rage kuɗin sarrafa kayayyaki a gida, muna ƙarfafa masana'antun cikin gida."
"Muna bayar da duk wani tallafi domin kowa ya bi ƙa’ida. Allah ya albarkaci ƙasarmu, Allah ya albarkaci jihar Legas, ya kuma kare sojojinmu masu fafatawa a fagen daga."

Kara karanta wannan

Nuhu Ribadu ya koka kan rashin tsaro, ya fadi adadin 'yan Najeriya da matsalar ta shafa

- Shugaba Bola Tinubu

Shugaba Bola Tinubu
Tinubu ya ce yana sane da tsammanin da ake yi masa Hoto: Ibrahima Kaulaha Mohammed
Source: Facebook

Tinubu ya ja kunnen masu gine-gine

Shugaban ƙasan ya kuma gargaɗi masu gina gine-gine, yana cewa yin gini a fili ba tare da samun amincewa ba, ba za a biya masa diyya ba.

"Ina so na gargaɗi duk masu gine-gine, Gwamnatin Tarayya ta ƙarfafa tsarin tsaftace filaye domin amfanin ƙasa baki ɗaya. Duk wani gini da ba a amince da shi ba, ba za a biya diyya ba."
"Mun riga mun fitar da tsarin, mun wallafa shi, kuma za mu tabbatar da ana bin sa a ko'ina."

- Shugaba Bola Tinubu

An wahalar da ƴan Najeriya

Auwal Kabir ƴa shaidawa Legit Hausa cewa kullum zancen da gwamnati ke yi kenan a yi haƙuri alhalin mutane na cikin shan wahala.

"Mutane na shan wahala yayin da shugabanni kuma ke ta fantamawa. Sannan a haka sai a fito a ce a yi haƙuri."

"Magana ta gaskiya gwamnati ba ta damu da halin da mutane suke ciki ba, don da ta damu da an nemawa jama'a hanyar neman samun sauƙi."

Kara karanta wannan

Jami'an DSS da sojoji sun yi rubdugu kan 'yan bindiga, an kashe miyagu da dama

"Wannan gwamnatin ta wahalar da ƴan Najeriya tare da jefa su cikin mawuyacin hali."

- Auwal Kabir

Amaechi ya ce bai goyi bayan Tinubu ba

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya bayyana cewa bai goyi bayan Shugaba Bola Tinubu ba a zaɓen 2023.

Amaechi ya bayyana cewa ya gayawa Tinubu cewa ba zai goya masa baya ba, kuma ba zai zaɓe shi ba a zaɓen 2023.

Tsohon gwamnan na jihar Rivers ya ce ya yi hakan ne domin bai yi amanna kan cewa Tinubu yana da ƙwarewar da zai jagoranci Najeriya ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng