"Sun cika Mantuwa": Hadimin Tinubu Ya Caccaki Masu Sukar Shugaban Kasa

"Sun cika Mantuwa": Hadimin Tinubu Ya Caccaki Masu Sukar Shugaban Kasa

  • Hadimin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi magana kan.masu sukar ubangidansa kan halin da ƙasar nan take ciki
  • Bayo Onanuga ya bayyana cewa masu ɗora alhaki kan shugaban ƙasan suna da saurin manta abubuwa
  • Ya bayyana cewa kafin Shugaba Tinubu ya hau kan karagar mulki, abubuwa da dama sun taɓarɓare a ƙasar nan

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Mai ba Shugaba Bola Tinubu shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya yi magana kan masu sukar shugaban ƙasa.

Bayo Onanuga ya ce dalilin da yasa mutane da dama ke ɗora laifi ga Tinubu kan matsalolin ƙasar nan shi ne saboda suna da saurin mantuwa wanda hakan ya sanya suka manta da halin da ƙasar take ciki kafin ya hau mulki.

Kara karanta wannan

Nuhu Ribadu ya koka kan rashin tsaro, ya fadi adadin 'yan Najeriya da matsalar ta shafa

Bayo Onanuga
Bayo Onanuga ya kare Shugaba Tinubu Hoto: @aonanuga1956
Source: Facebook

Bayo Onanuga ya faɗi hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a tashar Arise Tv a ranar Juma’a, 30 ga watan Mayun 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Onanuga ya soki masu sukar Tinubu

Ya ce mutane na gaggawar ɗora laifi kan gwamnatin yanzu ba tare da tuna halin da ƙasar ke ciki kafin Shugaba Tinubu ya hau mulki ba.

“Bari na fara da cewa mu da yawa a wannan ƙasa, ƴan Najeriya da yawa muna da wata matsala ta saurin mantuwa. Muna da saurin manta abin da ya faru a baya."
“Mun manta da inda muka fito, sai kawai mu fara ɗorawa Shugaba Tinubu laifin duk wata matsala da Najeriya ke fuskanta."

- Bayo Onanuga

Ya tunatar da cewa Najeriya tana fuskantar matsalar ƙarancin man fetur kafin Shugaba Tinubu ya hau mulki a watan Mayu 2023.

Ya ce ƙarancin man ya yi ƙamari watanni kafin babban zaɓe, inda aka ga layuka masu tsawo a gidajen mai a faɗin ƙasar.

Kara karanta wannan

"Ya gaza": Tsohon gwamna ya caccaki Tinubu kan kuntatawa 'yan Najeriya

Onanuga ya faɗi matsalolin da aka baro baya

A cewarsa, kamfanin man fetur na ƙasa (NNPCL), wanda shi kaɗai ne ke shigo da mai a lokacin, ya rage shigo da man ne saboda yana bin gwamnatin tarayya bashin fiye da N4trn na kuɗin tallafin da ba a biya ba.

Ya ce a irin wannan mawuyacin hali ne Tinubu ya sanar da cire tallafin man fetur a ranar farko da ya hau mulki.

Wannan matakin ya jawo tashin farashin mai, tare da yunƙurin gwamnati na dawo da wadatar mai a ƙasar.

Bayo Onanuga
Onanuga ya soki masu caccakar Tinubu Hoto: @aonanuga1956
Source: UGC
"Ina tunawa cewa, misali a watan Mayun 2023 lokacin da Tinubu ya karɓi mulki, akwai ƙarancin mai a wannan ƙasa."
“Mutane sun manta cewa a lokacin zaɓen shekarar nan gaba ɗaya, akwai ƙarancin man fetur. Saboda haka yana hawa mulki, ya sanar da cire tallafin mai a ranar farko."

- Bayo Onanuga

Onanuga ya ce mutane na mantawa da waɗannan abubuwa cikin sauƙi. Ya jaddada cewa Najeriya ba za ta iya ci gaba da ɗaukar nauyin tallafin mai ba, saboda ƙasar ba ta da isassun kuɗaɗe.

Kara karanta wannan

Malamin addini ya fito karara ya gayawa Tinubu abin da zai hana shi tazarce a 2207

An ba Tinubu ragon layya

A wani labarin kuma, kun ji cewa wani matashi daga jihar Bauchi, ya ba Shugaba Bola Tinubu kyautar ragon layya.

Matashin mai suna Khamis Musa Darazo ya bayyana cewa ya yi kyautar ne ga shugaban ƙasan saboda ba da lasisin aikin haƙo mai a Kolmani.

Ya nuna cewa aikin zai buɗe hanyoyin samun kuɗi ga matasa a Arewacin Najeriga

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng