DisCos Sun Lafto Kudin Shan Wuta, Mataimakin Gwamna Ya Koka da Tsadar Lantarki
- Mataimakin Gwamnan Legas ya bayyana takaicinsa kan yadda kamfanin EKEDC ya turo masa da kudin lantarki har N29m a watan Afrilu
- Obafemi Hamzat ya ce wannan ya ninka abin da aka aiko masa a watan baya, inda aka bukaci ya biya N2.7m na kudin wutar da ya sha
- Hamzat ya ce matsalar lantarki da aringizo ba wai manyan jami'an gwamnati kaɗai ke fama da ita ba, har da talakawa da 'yan kasuwa a
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Mataimakin Gwamnan jihar Legas, Obafemi Hamzat, ya nuna damuwa kan abin da ya kira aringizon kudin wutar lantarki daga kamfanonin rarraba lantarki a Najeriya.
A cewarsa, an turo masa da kudin wutar lantarki na Naira miliyan 29 a watan Afrilu kawai — lamarin da ya haura 10% na abin da aka turo masa a watan Maris, wanda ya kasance N2.7m.

Asali: Twitter
Premium Times ta wallafa cewa, Hamzat ya bayyana hakan ne yayin taron tattaunawa tsakanin gwamnatin Legas da hukumar kula da wutar lantarki a karkara (REA), da aka gudanar a jihar a ranar Litinin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kamfanin lantarki ya fusata mataimakin gwamna
Jaridar Punch ta ruwaito cewa Hamzat ya bayyana yadda kamfanin Eko Electricity Distribution Company (EKEDC) ya hana shi amfani da mita duk da cewa ya riga ya biya kudinta.
Ya ce:
“Watan da ya gabata, an turo min da kudin lantarki na Naira miliyan 2.7. Amma wannan watan, Eko DisCo sun turo min da Naira miliyan 29.
"Na turawa Kwamishinan Makamashi don ya duba lamarin. Wannan hauka ne. Na siya mita don guje wa tsarin aringizon kudin lantarki, amma har yanzu an hana ni."
Hamzat, wanda ya wakilci Gwamna Babajide Sanwo-Olu a taron, ya ce matsalar lissafin wutar lantarki ba ta takaita ga manyan jami’an gwamnati kadai ba, har da talakawan Legas.
Lantarki: An shiga yarjejeniga da gwamnatin Legas
A taron, an samu damar rattaba hannu a kan wata yarjejeniyar fahimtar juna (MoU) tsakanin gwamnatin Legas da REA don kai haske kauyukan jihar ta hanyar amfani da hasken rana.

Asali: Facebook
Kwamishinan makamashi da albarkatun ƙasa, Biodun Ogunleye, ya yaba da hadin gwiwar, yana mai cewa wannan babbar dama ce da za ta samar da wutar lantarki mai dorewa ga al’ummarsu.
Ya ce:
“Ana buɗe ƙofofi ga mutane da dama da ba su taɓa tunanin za su samu wutar lantarki mai ɗorewa ba.”
A bangarensa, Daraktan gudanarwa na REA, Abba Aliyu, ya bayyana cewa hukumar ta gano wasu al’ummomi da za su ci gajiyar wannan shiri a kauyuka.
Ya ce daga cikin shirin, akwai gina wani ƙaramin kamfanin samar da wutar hasken rana mai ƙarfin megawatt 8 a Jami’ar Legas — wanda har yanzu yana jiran amincewar gwamnatin jihar.
Za a dakatar da samar da wutar lantarki

Kara karanta wannan
Portable: Ƴan sanda sun kama fitaccen mawakin Najeriya, an ji laifin da ya aikata
A baya, kun ji cewa kamfanonin samar da wutar lantarki a Najeriya, wato GenCos, sun fitar da sanarwa mai ɗauke da gargaɗi, kan samar da wutar lantarki a kasa.
Sun bayyana cewa za su dakatar da ayyukansu nan gaba kadan, idan gwamnatin tarayya ta ci gaba da yin biris da biyan su bashin da ya kai N4trn, kuma ya hana su aikinsu.
Shugaban kwamitin amintattun GenCos, Kanal Sani Bello (mai ritaya), ya ce kamfanonin sun shiga mawuyacin hali, kuma suna ci gaba da gudanar da ayyukansu tare da fuskantar kalubale iri-iri.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng