Matakin da Gwamnan Edo Ya Dauka kan Kisan Gillar da Aka Yi Wa 'Yan Arewa
- Gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo ya ɗauki mataki kan kisan gillar da aka yi wa mafarauta ƴan Arewa a kan hanyarsu ta komawa Kano
- Monday Okpebholo ya dakatar da kwamandan rundunar tsaron jihar sabida ɗanyen aikin da aka aikata kan mafarautan
- Gwamnan ya kuma bayyana cewa ƴan sa-kan da suka tare mafarautan, ba su da rajista da hukumomin jihar
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Edo - Gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo, ya fara ɗaukar mataki kan kisan da aka yi wa mafarauta ƴan Arewa a jihar.
Gwamna Monday Okpebholo ya dakatar da kwamandan rundunar tsaron Edo, Friday Ibadin, saboda kisan gillar da aka yi wa mafarauta 16 a yankin Uromi na jihar.

Asali: Twitter
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar ya fitar a ranar Asabar, cewar rahoton jaridar TheCable.

Kara karanta wannan
"Ba yau aka fara ba," Gwamnatin Kano ta yi zazzafan martani kan kisan ƴan Arewa a Edo
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wane mataki gwamnan Edo ya ɗauka?
Gwamna Okpebholo ya kuma bayar da umarnin dakatar da ƙungiyoyin sa-kai marasa rajista da ke aiki a jihar.
A ranar Alhamis, wasu gungun mutane a yankin Uromi na Edo sun kashe mafarauta 16 ƴan Arewa yayin da suke tafiya daga Elele na jihar Rivers zuwa Kano.
Ƴan sanda sun bayyana cewa an kashe mafarautan ne bayan wata ƙungiyar sa-kai ta yankin ta zarge su da kasancewa masu garkuwa da mutane, bayan da ta gano bindigogin farauta 19 a tare da su.
Shugaba Bola Tinubu ya bayar da umarni ga ƴan sanda da hukumomin tsaro da su gudanar da bincike cikin gaggawa tare da gurfanar da masu laifin gaban shari’a.
Ƴan sa-kai ba su da rajista
A cikin sanarwar, gwamnan Edo ya ce kungiyar sa-kai da ta aikata wannan ɗanyen aiki ba ta da rajista kuma ba ta aiki a ƙarƙashin rundunar tsaron jihar Edo.

Asali: Twitter
"Yana da kyau a nanata cewa ƙungiyar sa-kai da ta aikata wannan kisan gilla a ranar 27 ga Maris tana aiki ne ba bisa ƙa’ida ba, domin ba a taɓa yi mata rajista ko tantance ta a ƙarƙashin rundunar tsaron jihar Edo ba."
"Ayyukanta ba su yi daidai da manufofin mulkin Okpebholo ba, ko kuma manufofin rundunar tsaro kamar yadda dokar tsaro ta jihar Edo ta tanada."
"Ana ci gaba da bincike kan kisan, kuma tuni an kama mutane 14, yayin da ake ci gaba da farautar sauran da suke da hannu a wannan ɗanyen aiki, tare da haɗin gwiwar wata tawaga ta musamman da sufeto janar na ƴan sanda ya kafa."
"Gwamnatin jihar Edo tana nan kan bakanta na kare ƴancin dukkan ƴan ƙasa kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada, don su yi rayuwa cikin ƴanci kuma su gudanar da kasuwanci ba tare da tsangwama ba a kowane yanki na ƙasar nan."

Kara karanta wannan
Kisan 'rashin imani' da aka yi wa 'yan Arewa ya tada ƙura, Kwankwaso ya maida martani
"A halin yanzu, gwamnatin jihar tana tuntubar iyalan waɗanda suka rasa rayukansu, shugabannin al’umma, da kuma gwamnatin jihar Kano, inda yawancin mamatan suka fito."
- Sakataren gwamnatin Edo
Babban hafsan tsaro ya magantu kan kisan Edo
A wani labarin kuma, kun ji cewa babban hafsan hafsoshin tsaron ƙasa, Janar Christopher Musa, ya yi Allah wadai kan kisan da aka yi wasu mafarauta ƴan Arewa a jihar Edo.
Janar Christopher Musa ya miƙa saƙon ta'aziyyarsa ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da iyalan mutanen da suka rasa rayukansu.
Asali: Legit.ng