Babbar Magana: Izala za Ta Maka Dan Bello a Kotu kan Zargin Sheikh Bala Lau
- Kungiyar Izala ta ce za ta gurfanar da Dan Bello a kotu kan zarge-zargen da ya yi wa shugabanta, Sheikh Abdullahi Bala Lau
- Kungiyar ta musanta cewa ta karɓi kuɗi daga gwamnatin tarayya domin gina ajujuwa, tana mai cewa ayyukan wasu ‘yan majalisa ne
- Izala ta ce Dan Bello ya yi sharrin da ke da nufin ɓata sunan shugabanta da ƙungiyar, don haka za ta bi hakkinta ta hanyar shari’a
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatus Sunnah (JIBWIS) ta bayyana cewa za ta maka Dan Bello a kotu bisa zargin ɓata sunan shugabanta, Sheikh Abdullahi Bala Lau.
Izala ta musanta zargin da Dan Bello ya yi cewa kungiyar ta karɓi kuɗi daga gwamnatin tarayya domin gina ajujuwa amma ba ta aiwatar da aikin ba.

Kara karanta wannan
Sanatocin Arewa sun haɗa kai, sun taso da ƙarfi kan abin da aka yi wa ƴan Arewa a Edo

Asali: Facebook
A sanarwar da kungiyar ta fitar a Facebook, ta bayyana cewa gine-ginen da ake magana a kansu suna karkashin ayyukan wakilan majalisar tarayya ne, ba kuɗin da aka bai wa kungiyar ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Izala ta musanta zargin Dan Bello
Kungiyar Izala ta ce Dan Bello ya yi kuskure wajen fassara bayanan ayyukan gine-ginen da wasu ‘yan majalisa suka shirya a makarantu daban-daban, ciki har da na Izala.
Ta bayyana cewa aikin gine-ginen da ake magana a kai na daga cikin ayyukan dan majalisar tarayya, Hon. Mukhtar Aliyu Betara, mai wakiltar Bayo/Biu/Kwaya-Kusar a majalisar wakilai.
Haka nan, akwai wani aikin da aka yi a kwalejin ilimi ta JIBWIS da ke Jega a jihar Kebbi, wanda shi ma na wani dan majalisa ne, Sanata Muhammad Adamu Aliero.
Izala ta ce ba a bai wa kungiyar kuɗi domin aiwatar da wadannan ayyuka ba, illa dai ‘yan majalisar ne suka shirya su kuma suka aiwatar da su a wuraren da suka dace.

Kara karanta wannan
Kungiyar Izalah ta yi maganar kisan ƴan Arewa a Edo, ta fadi hanyar dakile lamarin

Asali: Facebook
Izala ta ce Dan Bello ba shi da hujja
Kungiyar ta ce duk zarge-zargen da Dan Bello ke yi kan Sheikh Abdullahi Bala Lau na neman a bata masa suna ne kawai, ba tare da wata hujja ba.
Ta kara da cewa zargin cewa shugabanta yana da asusun banki fiye da guda 30 ba gaskiya ba ne, don haka ta bukaci Dan Bello ya gabatar da cikakken bayani da shaidu kan hakan.
Haka nan, Izala ta ce babu wata hujja da ke nuna cewa Sheikh Abdullahi Bala Lau yana da wani ofishi na kungiya a Lau, jihar Taraba, kamar yadda Dan Bello ya fada.
Izala za ta maka Dan Bello a kotu
Kungiyar Izala ta bayyana cewa bayan mika karar Dan Bello ga Allah, yanzu za ta dauki matakin shari’a domin kare martabar shugabanta da kungiyar.

Kara karanta wannan
"Ba yau aka fara ba," Gwamnatin Kano ta yi zazzafan martani kan kisan ƴan Arewa a Edo
A cewar kungiyar, za su gurfanar da shi a kotu domin ya fitar da hujjojin da ke tabbatar da zarge-zargen da ya yi.
Ta ce ko hukuma ce za ta gudanar da bincike kan BVN ko wasu bayanai na sirri, dole sai da izini daga mahukunta.
Kungiyar ta ce lokaci ya yi da za a kawo karshen irin wadannan zarge-zarge na karya da kuma yunkurin bata sunan malamai da kungiyoyin addini.
Yanzu dai za a jira ganin yadda shari’ar za ta kaya da kuma yadda Dan Bello zai kare kansa a gaban kotu.
Hukuncin rama sallar Idi a Musulunci
A wani rahoton, kun ji cewa marigayi Sheikh Dr Ahmad Bamba ya taba yin bayani kan yadda ake rama sallar Idi.
Dr Ahmad ya bayyana cewa ya halasta mutum ya rama sallar Idi idan ya makara, kuma mutum zai iya rama sallar a gida ko a masallaci.
Asali: Legit.ng