Bianca: Ministar Tinubu Ta Tuna Baya, Ta Fadi Yadda Mahaifinta Ya Koreta daga Gida
- Bianca Odumegwu-Ojukwu ta tuna baya kan irin gwagwarmayar da ta sha a baya a rayuwarta lokacin da take matashiya
- Ƙaramar ministar harkokin wajen ta Najeriya ta bayyana akwai lokacin da mahaifinta ya taɓa korarta daga gida saboda ta shigar gasar kyau
- Ta nuna muhimmancin ilmi ga rayuwar mace inda ta ba da shawarar cewa ka da ƴan mata su riƙa kyale karatu bayan sun fara samun kuɗi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Birnin New York - Ƙaramar ministar harkokin wajen Najeriya, Bianca Odumegwu-Ojukwu, ta nuna baya kan yadda aka kore ta daga gida.
Bianca Ojukwu ta bayyana cewa mahaifinta ya kore ta daga gida ne saboda ta shiga gasar sarauniyar kyau.

Asali: Twitter
Ta yi wannan bayani ne a ranar mata ta Najeriya, a gefen taro kashi na 69 na hukumar kare hakkin mata a hedkwatar majalisar ɗinkin duniya da ke birnin New York, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Kara karanta wannan
Kurunkus: Bayanai sun fito kan zargin ba kowane dan majalisa $5000 don Amincewa da dokar ta baci
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bianca Ojukwu, wacce mahaifinta ya taɓa zama gwamna a Najeriya, ta ce a matsayin ta na matashiya, ba ta bari gata da jin daɗin da iyayenta suka ba ta sun shagaltar da ita ba.
Bianca Ojukwu ta faɗi muhimmanci ilmi ga mata
Ta jaddada mahimmancin ilimi a rayuwar kowace mace, tana mai cewa a lokacin da ta fara samun kuɗi a matsayin sarauniyar kyau, ta yi fama da ruɗin barin karatunta na lauya a jami’ar Najeriya, da ke Enugu, rahoton The Nation ya tabbatar.
"Na fara ne a matsayin wata ƴar yarinya da ke son ganin duniya."
"Ina tuna lokacin da muke zama a ɗakin taro tare da sauran ƴan mata, muna kallon fina-finai da gasar kyau irin su Miss World da Miss Universe. Mafi yawa abin da ke burge mu shi ne kyawawan wuraren da ake gudanar da gasar."
"Ni kuma na ce wa kaina, me zai hana na shiga gasar kyau domin samun damar yin yawo a duniya?"
"Tabbas, iyayena ba su san niyyata ba. Ba su tura ni makaranta don na shiga gasar kyau ba, don haka dole na haƙura da shi."
"Sai da na shiga gasar sarauniyar kyau ta Najeriya sannan na fuskanci matsala. Har aka kore ni daga gida tsawon wata guda saboda mahaifina kamar sauran iyaye ƴan Afirika, ya fusata matuƙa."
"Amma daga baya, bayan na lashe wasu gasa kamar Miss Africa da Miss Intercontinental, dole ya haƙura."
"Abin da nake ƙoƙarin nunawa shi ne, ɗaya daga cikin manyan ƙalubalen da matasa ke fuskanta shi ne idan suka fara samun kuɗi da wuri, suna iya barin makaranta."
"Lokacin da na fara samun kuɗina, ɗaliba ce ni a fannin Shari’a, ina zaune a cikin ɗakin kwana tare da wasu ƴan mata shida, babu ruwa, babu komai. Amma sai na yanke shawarar dawowa don kammala karatuna."
"Hakan na ɗaya ne daga cikin mafi kyawun shawarwarin da na taɓa yanke a rayuwata. Ina ganin dole ƴan mata su fahimci muhimmancin ilimi da irin ikon da yake da shi a rayuwa."
- Bianca Odumegwu-Ojukwu
Bianca Ojukwu ta roƙi Tinubu kan Nnamdi Kanu
A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙaramar ministar harkokin wajen Najeriya, Bianca Odumegwu-Ojukwu na son Shugaba Bola Tinubu ya saki Nnamdi Kanu.
Bianca Ojukwu ta bayyana za ta ci ga da roƙon shugaban ƙasan domin ya saki jagoran na ƙungiyar ƴan aware ta IPOB.
Asali: Legit.ng