Hadimin Gwamna Ya Shiga Fadar Gwamnati Ɗauke da Maciji, Manyan Mutane Sun Tsure

Hadimin Gwamna Ya Shiga Fadar Gwamnati Ɗauke da Maciji, Manyan Mutane Sun Tsure

  • Mutane sun firgita da hadimin gwamnan Kebbi, Kabir Sani-Giat ya shiga da maciji gidan gwamnati da ke Brinin Kebbi
  • Jam'iyyar APC ta dakatar da hadimin gwamnan nan take, ta ce ba za ta lamunci duk wani abu da zai sa ta ji kunya ba
  • Sakataren APC, Sa'idu Muhammad ya ce an dakatar da Kabir har sai an kammala bincike kan abin da ake zargin ya aikata

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kebbi - Mai ba gwamnan jihar Kebbi, Nasiru Idris shawara ta musamnan kan harkokin makamashi da siyasa, Kabir Sani-Giant ya jefa kansa cikin matsala.

Hadimin gwamnan ya shigar da maciji gidan gwamnatin Kebbi da ke Birnin Kebbi, lamarin da ya harzuƙa jam'iyyar APC mai mulki.

Dr. Nasir Idris.
APC ta dakatar da hadimin gwamna bisa tsorata mutane da maciji a gidan gwamnatin Kebbi Hoto: Dr. Nasir Idris Kauran Gwandu
Asali: Facebook

Kamar yadda Premium Times ta ruwaito, APC ta sanar da dakatar da Kabir Sani Giat daga jam'iyyar bisa wannan ɗabi'a da ta ce ta saɓawa kundin tsarin mulkinta.

Kara karanta wannan

Ana ciyar da mabukata a Kano, mutane 91,000 za su samu buda-bakin Ramadan

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

APC ta dakatar da hadimin gwamnan Kebbi

Hakan dai na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren jam’iyyar APC na jihar Kebbi, Sa’idu Muhammad-Kimba, ya fitar a ranar Lahadi a Birnin Kebbi.

Ya bayyana cewa an dakatar da Sani-Giant nan take, har sai an kammala bincike kan abin da ya aikata wanda ya jawo muhawara mai zafi a APC da gwamnatin Kebbi.

A cewar Sa'idu, a ranar 8 ga Fabrairu 2025, Sani-Giant ya shigar da maciji cikin fadar gwamnatin jihar Kebbi, wanda hakan ya firgita manyan baki, dattawa da jami’an gwamnati da ke wurin a lokacin.

Dalilan dakatar da hadimin gwamna

Sanarwar ta bayyana cewa irin wannan ɗabi’a ba ta dace da matsayin da Kabir Sani-Giant ke rike da shi ba, domin yana iya zubar da mutuncin gwamnatin jihar da jam’iyyar APC baki ɗaya.

“Shigar da maciji cikin fadar gwamnati ya haifar da firgici ga mutane da dama, ciki har da manyan jami’an gwamnati da ‘yan siyasa.

Kara karanta wannan

Dalibai sun fusata kan rufe makarantu a Arewa, NANS ta shirya zanga-zanga

"Wannan aiki ya saba wa dokokin jam’iyyar APC kuma yana iya haifar da abin kunya da tozarta,” in ji Sa'idu Muhammad

APC ta fara gudanar da bincike

Bisa la’akari da girman abin da ya aikata, APC ta ce dakatarwar na wucin gadi ne har sai an kammala bincike mai zurfi.

Idan har aka tabbatar da cewa laifinsa ya yi muni fiye da yadda ake tunani, yana iya fuskantar kora gaba ɗaya daga jam’iyyar APC.

Jam'iyyar APC.
APC ta fara gudanar da bincike kan shigar da maciji gidan gwamnatin Kebbi Hoto: APC Nigeria
Asali: Getty Images

Jam’iyyar ta kara da cewa tana da kyakkyawan tsarin ladabtar da ‘ya’yanta da ke aikata abubuwan da ke iya rage martabarta.

Jam’iyyar APC ta jaddada cewa ba za ta lamunci duk wani abu da zai kawo mata koma baya ko zubar mata da mutunci ba.

Ta gargadi dukkan ‘ya’yanta da su guji aikata abubuwan da za su iya haifar da rikici ko jefa jam’iyyar APC cikin abin kunya.

Gwamnan Kebbi ya kori mutum 21 daga aiki

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta ware kudin ciyarwa a Ramadan, ta fadi abin da za ta kashe

A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Nasir Idris (Kauran Gwandu) ya kori dukkan shugabannin hukumomin ilimi na kananan hukumomin 21 da ke jihar Kebbi.

Gwamnan Kebbi ya yaba da gudunmuwar da wadannan shugabanni suka bayar wajen ci gaban ilimi a yankunansu, tare da yi musu fatan alheri.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262