Buhari Ya Yi Karin Haske kan Komawa Kaduna da Gidan da Ya ba da Haya
- Tsohon Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari, ya koma gidansa da ke Kaduna bayan shafe lokaci a Daura tun bayan barinsa mulki
- ‘Yan Najeriya sun bukaci Muhammadu Buhari ya yi bayani kan gidan da ya bayar haya a Kaduna bayan da aka ga ya koma jihar da zama
- Tsohon hadiminsa, Bashir Ahmad, ya yi bayani kan gidajen da tsohon shugaban kasar ya mallaka da gidan da ya ba da haya a Kaduna
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kaduna - Tsohon Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari, ya koma Kaduna bayan shafe lokaci a mahaifarsa ta Daura, Jihar Katsina tun bayan kammala wa’adinsa na mulki.
Gwamnan Kaduna, Uba Sani, ya ce ya yi farin cikin tarbar Muhammadu Buhari zuwa Kaduna, yana mai yi masa fatan zama lafiya a cikin birnin da yake matukar kauna.

Asali: Twitter
Tsohon hadimin shugaban, Bashir Ahmad ya yi karin haske a Facebook kan tambayoyi da jama'a suka yi a kan komawar Buhari Kaduna kasancewar ya taba cewa ya ba da gidansa na jihar haya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Manyan mutane a Najeriya ne suka raka Buhari zuwa gidansa da ke Kaduna, ciki har da Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, da Gwamnan Borno, Babagana Zulum.
‘Yan Najeriya sun bukaci Buhari ya yi bayani
Bayan labarin komawarsa Kaduna, ‘yan Najeriya da dama sun bukaci Buhari ya fayyace batun gidan da ya bayar haya domin samun kudin shiga.
Tun da farko, tsohon Shugaban Kasar ya ce yana samun kudin shiga ne daga hayar daya daga cikin gidajensa da ke Kaduna.
Wannan bayani ya jawo tambayoyi daga wasu da suka bukaci karin haske kan ko yana da wani wuri a Kaduna bayan ba da gidan haya.

Asali: Twitter
Bashir Ahmaad ya fayyace batun gidajen Buhari
Hadimin tsohon Shugaban Kasa, Bashir Ahmad, ya bayyana cewa Buhari na da gidaje biyu a Kaduna, inda daya daga cikinsu ya bayar haya, amma yana da wani da yake zaune a ciki.
A cewarsa, Buhari ya tabbatar da cewa bayan kammala wa’adinsa a mulki, ya mallaki gidaje uku kacal: Daya a Daura da biyu a Kaduna.
Bashir Ahmad ya ce wannan ya wanke duk wata tantama kan ko Buhari yana da wurin zama a Kaduna ko a’a.
"Ga wadanda suka shiga rudani a kan komawar tsohon shugaban kasa gidansa na Kaduna bayan ya ce ya bayar da hayan gidansa na jihar a kwanan nan.
Buhari yana da gidaje biyu a jihar Kaduna kamar yadda da kansa ya ce yana da gidaje biyu a Kaduna, daya a Daura bayan kammala shugabancin Najeriya na shekaru 8.
"Saboda haka, har yanzu ya bayar da hayar gidansa na Kaduna guda daya yayin da zai zauna a daya gidan."
- Bashir Ahmad
Muhammadu Buhari bai je taron APC ba
A wani rahoton, kun ji cewa shugaba Muhammadu Buhari ya yi magana bayan rashin halatar babban taron APC a birnin Abuja.
Tsohon shugaban kasar ya bayyana cewa bai samu gayyata da wuri ba ne amma har yanzu yana matsayin cikakken dan jam'iyyar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng