Jami'an Tsaro Sun Toshe Titunan Zuwa Fadar Aminu Ado Bayero a Kano, an Gano Dalili
- Dakarun ƴan sanda da sauran jami'an tsaro sun tsaurara matakan tsaro a titin zuwa fadar Nasarawa, wurin da sarki na 15, Aminu Ado Bayero yake zaune
- Rahotanni sun nuna cewa jami'an tsaron sun toshe dukkan hanyoyin da ke kai wa zuwa ƙaramar fadar Nasarawa
- Mai magana da yawun ƴan sandan Kano, SP Haruna Kiyawa ya ce sun ɗauki wannan matakin ne bayan samun labarin za a yi zanga-zanga
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano - Jami’an tsaro sun toshe titunan zuwa karamar fadar sarkin Kano da ke Nasarawa, wurin da sarki na 15, Aminu Ado Bayero, ke zaune.
Wannan mataki ya haddasa cece-kuce da rade-radi a tsakanin jama’a, inda mutane ke kokwanto kan abin da ke faruwa.

Asali: Twitter
Ganau sun bayyana cewa hanyoyi da dama da ke kaiwa fadar an toshe su a yau Laraba, 26 ga watan Fabrairu, 2025, kamar yadda Leadership ta tattaro.

Kara karanta wannan
Jama'a suna zaman ɗar-ɗar, jami'an tsaro da sulken yaki sun kewaye gidan sarki a Kano
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jami'an tsaro sun hana bin titin gidan sarki
An ruwaito cewa jami’an tsaro suna tilasta wa masu ababen hawa bin wasu hanyoyin daban wanda hakan ya haddasa cunkoso da wahalar zirga-zirga a yankin.
Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa manema labarai cewa:
"Mun saba ganin jami’an tsaro a kusa da fadar, amma wannan karon sun tsaurara matakan tsaro fiye da kowane lokaci. An hana mutane shiga da fita, kuma motoci ba sa iya ketarawa ta wadannan hanyoyi."
Idan baku manta ba Kano na fama da rikicin sarauta tun da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya tsige Aminu Ado Bayero tare da maido da Muhammadu Sansui II kan mulki.
Yan sanda sun faɗi dalilin ɗaukar matakin
Da yake bayani kan lamarin, mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Kano, SP Abdullahi Kiyawa, ya ce an dauki wannan mataki ne bayan samun bayanan sirri.
A cewarsa, sun samu labarin wasu gungun mutane na shirin gudanar da wata zanga-zangar tarzoma a Kano.
"Bayan mun samu sahihan rahotanni cewa ana shirin tayar da fitina, mun dauki matakin tura jami’ai da kayan aiki zuwa wurare masu muhimmanci a cikin birnin Kano don tabbatar da tsaro da kare rayuka da dukiyoyi."
Haka nan, ‘yan sanda sun kama mutum 17 da ake zargin ‘yan daba ne, kuma ana ci gaba da bincike a kansu.
Yan sanda sun gargaɗi jama'a
SP Kiyawa ya jaddada cewa duk wanda aka samu da laifin haddasa hargitsi ko tada zaune-tsaye zai fuskanci hukunci daga hukumomin tsaro.
Ya gargadi dukkan jama’a da kungiyoyin da ke shirin yin taruka ko gangami na bore ba tare da izini ba, cewa duk wanda ya saba doka ba zai tsira ba.
"Duk wani mutum ko kungiya da ke shirin tayar da tarzoma zai gamu da hukunci. Muna kira ga jama’a da su kwantar da hankalinsu su kuma guji shiga duk wata fitina," in ji SP Kiyawa.
Har yanzu dai babu wata sanarwa daga bangaren Aminu Ado Bayero ko magoya bayansa dangane da wannan matakin tsaro da aka dauka a kusa da fadarsa.
Aminu Ado ya gana da Bola Tinubu
Kun ji cewa sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero ya gana da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, jim kaɗan kafin ya tashi zuwa ƙasar Faransa.
Sanarwar da ta fito daga ɓangaren basaraken ta nuna cewa tattaunawar ta shafi rikicin da ya faru a Rimin Zakara a Ungogo da ke jihar Kano.
Asali: Legit.ng