Attahiru Jega Ya Gano Matsalar Dimokuradiyya a Afirika, Ya Fadi Mafita

Attahiru Jega Ya Gano Matsalar Dimokuradiyya a Afirika, Ya Fadi Mafita

  • Tsohon shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya (INEC) ya taɓo batun juyin mulkin da ake samu a yankin Afirika ta Yamma
  • Attahiru Jega ya bayyana cewa dimokuraɗiyya na ja da baya a yankin sakamakon riƙon sakainar kashi da shugabanni suke yi wa amanar da aka ba su
  • Farfesan ilmin siyasar ya yi kira da a gaggauta kawo sababbin tsare-tsare waɗanda za su tabbatar da cewa zaɓe ya yi daidai da ra'ayin jama'a

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Tsohon shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC), Attahiru Jega ya yi magana kan dimokuraɗiyya a yankin Afirka ta Yamma.

Attahiru Jega ya bayyana cewa dimokuraɗiyya na ja da baya a yankin sakamakon gazawar gwamnati da kuma shugabanci mara kyau.

Jega ya koka kan tabarbarewar dimokuradiyya a Afirika ta Yamma
Jega ya ce dimokuradiyya na ja da baya a Afirika ta Yamma Hoto: Stringer
Asali: Getty Images

Jaridar TheCable ta ce Jega ya yi wannan bayani ne a Abuja ranar Talata a matsayin babban mai jawabi a taron “Nazari kan zaɓen dimokuraɗiyya a Afirka ta Yamma,” wanda ƙungiyar Yiaga Africa, ta shirya.

Kara karanta wannan

Tsohon shugaban ƙasa, Jonathan ya fallasa yadda ake murɗe zaɓe a Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me Attahiru Jega ya ce kan dimokuraɗiyya?

Tsohon shugaban INEC ya ce gazawar gwamnati da shugabanci mara kyau suna haifar da juyin mulki a yankin.

"Waɗanda aka zaɓa a matsayin wakilan al’umma sun mayar da dukiyar jama’a tamkar mallakarsu, suna tarawa kansu arziƙi a maimakon su kula da buƙatu da muradun ƴan ƙasa."
"Rashin cimma nasarorin da ake sa ran samu a tsarin dimokuraɗiyya, wanda ke faruwa saboda waɗannan matsaloli, ya bai wa masu juyin mulki hujjar dawowa."
"Wannan yanayi mai haɗari na iya mamaye yankin kuma ya haifar da koma-baya a dimokuraɗiyya, sai dai idan an magance matsalolin yadda ya kamata cikin hanzari."

- Farfesa Attahiru Jega

Farfesa Jega ya lura cewa maimakon ƙarfafa dimokuraɗiyya, shugabanni da dama a yankin suna amfani da zaɓe a matsayin wata hanya ta cigaba da riƙe mulki.

"Zaɓe ya koma kamar wani shiri ne na kwaikwayo don tabbatar da ci gaba da zama kan mulki na shugaban ƙasa da jam’iyyarsa."

Kara karanta wannan

Daga karshe Shugaba Tinubu ya fadi kudaden da ake ba gwamnonin Najeriya

- Farfesa Attahiru Jega

Farfesa Jega ya soki siyasar ƙabilanci

Masanin ya kuma soki rawar da “siyasar bambancin ƙabila" ke takawa, yana mai gargaɗin cewa ƴan siyasa suna amfani da ƙabilanci da addini don cigaba da riƙe mulki, abin da ke ƙara tayar da rikici.

Tsohon shugaban INEC ya yi kira da a gaggauta yin garambawul domin ƙarfafa hukumomi, ƙarfafa riƙon amana, da tabbatar da cewa zaɓe na nuna sahihin ra’ayin jama’a.

Yadda Jega ya fallasa ƴan majalisar tarayya

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC), Farfesa Attahiru Jega, ya yi fallasa ga ƴan majalisar tarayya.

Farfesa Attahiru Jega ya bayyana cewa wasu ƴan majalisar tarayya na neman na goro domin su yi cushe a kasafin kuɗi.

Tsohon shugaban na hukumar INEC ya koka kan yadda ƴan majalisar suke takurawa masu riƙe da muƙamai domin ba su cin hanci.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng