Limami: "Abin da Ya Kamata Musulmai Su Yi Kafin a Fara Azumin Watan Ramadan"

Limami: "Abin da Ya Kamata Musulmai Su Yi Kafin a Fara Azumin Watan Ramadan"

  • Limamin masallacin FOMWAN Abuja, Sheikh Hayyatullahi Abdul-Ganiyi, ya nemi Musulmi su kara neman kusanci da Allah a Ramadan
  • Malamin ya ce sadaka, ciyarwa, da karatun Al-Qur’ani suna da girman lada, yana mai bukatar Musulmi su kara ninka ibada a watan
  • Ya bukaci Musulmi da su fara azumin Ramadan bayan sanarwar Sarkin Musulmi, tare da tabbatar da hadin kai da biyayya ga shugabanni

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - A yayin da Musulmi ke shirin Ramadan, babban limamin masallacin FOMWAN Abuja, Sheikh Hayyatullahi Abdul-Ganiyi, ya bukaci a koma ga Allah SWT.

Sheikh Hayyatullahi ya yi wannan kira ne yayin da yake gabatar da lakca ta gabatarwar Ramadan da aka shirya a birnin Abuja.

Limamin masallacin Abuja ya nemi Musulmi su nemi kusanci da Allah a Ramadan
Limami ya yi lakca kan falalar Azumi da abin da ake so Musulmi ya yi. Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Limami a Abuja ya yi lakcar azumi

Laccar mai taken “Juriya a Ramadan: Gina Da’a da Tsarkake Zuciya” ta jaddada mahimmancin wannan wata mai alfarma da ake tunkara, inji rahoton FRCN.

Kara karanta wannan

Ministan tsaro ya yi albashir ga Arewa kan matsalar ta'addanci, ya tabo alaka da Nijar

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin bayani kan Ramadan, malamin ya ce, "babban manufar azumi ita ce bauta wa Allah da kyakkyawan nufi, bayan tsarkake niyya."

Ya kara da cewa azumi yana koyar da hakuri, da’a, da tausayi ga mabukata, wanda ke inganta kyawawan halayen mai azumin.

'Musulmi su guji munanan ayyuka' - Limami

Sheikh Hayyatullahi ya ce Musulmi su guji duk wani abu da ka iya rage ladan azuminsu, kamar gaba da cin mutuncin mutane.

Ya jaddada cewa, "sadaka da kyautatawa ga mabukata na da girman lada, musamman a wannan wata mai daraja da za a shiga."

"Ciyar da mutane masu bukata yana daga cikin mafi girman ayyukan lada da ake bukata a yawaita yi lokacin Ramadan," inji Sheikh Hayyatullahi.

"Ku yawaita karanta Al-Qur’ani" - Limami

Sheikh Hayyatullahi ya bukaci Musulmi da su tsunduma cikin karatun Al-Qur’ani tare da nazarin ma’anar ayoyinsa.

Ya ce karatun Al-Qur’ani da lakantar manufofin ayoyi yana kara wa Musulmi fahimta da kusanci da Allah.

Kara karanta wannan

Zamfara: Sojoji sun lalata sansanin rikakken dan ta'adda, sun kwashe buhunan abinci

Malamin ya bukaci al’umma da su yawaita salloli, zikiri, da istigfari don samun rahamar Allah a watan Ramadan.

Limami ya fadi falalar biyayya ga shugabanni

Limami ya ba Musulmai shawarar ayyukan da za su yawaita yi a azumin Ramadan.
Limami a Abuja ya nemi Musulmai su yawaita karatun Al-Qur'ani, ciyarwa, da sadaka a Ramadan. Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Jaridar Daily Trust ta rahoto limamin ya kuma bukaci su yi amfani da Ramadan wajen gyara halaye da kauce wa duk wani abu na sabo.

Sheikh Hayyatullahi ya bukaci hadin kai da biyayya ga shugabannin addinin Musulunci domin samun nasarar yin ibada cikin tsari.

Ya bukaci Musulmi da su fara azumin Ramadan ne bayan sanarwa daga Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III.

Malamin ya ce, "biyayya ga shugabanni na tabbatar da hadin kan al’umma da zaman lafiya tsakanin Musulmi."

Limami ya nemi a taimakawa mabukata

Laccar ta zama tunatarwa kan muhimmancin bautar Allah, hakuri, da kyautatawa domin samun albarkar Ramadan.

Sheikh Hayyatullahi ya bukaci masu hali da su taimaka wa marasa karfi ta hanyar bayar da abinci da kayayyakin bukatu.

Ya ce, "taimakawa mabukata yana daga cikin hanyoyin samun lada mai yawa a wannan wata mai alfarma."

Kara karanta wannan

'Ya aikata laifuffuka 5': An gurfanar da fitaccen mawakin Najeriya a gaban kotu

Sheikh Hayyatullahi ya bukaci iyaye da su koya wa ‘ya’yansu darussan Ramadan domin su girma da kyakkyawan tarbiyya.

Ya ce Ramadan wata dama ce ta gyara rayuwa, tsarkake zuciya, da neman gafarar Allah cikin tsanaki.

Ramadan: Sanatan Kaduna zai raba N500m

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Sanata Lawal Usman zai rabawa 'yan mazabarsa ta Kaduna ta Tsakiya Naira miliyan 500 domin su wadata a azumin Ramadan.

Sanata Lawal ya ce tallafin kudin zai shafi har wadanda ba 'yan mazabarsa ba, ma damar Musulmai ne, yayin da ya nemi 'yan kasuwa su rage farashin abinci.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

iiq_pixel