"Najeriya Ta Yi Rashi": Atiku da Malam El Rufai Sun Sake Haɗuwa, Bidiyo Ya Bayyana
- Tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai ya shiga tawagar Atiku Abubakar, sun je ta'aziyya gidan marigayi Edwin Clark
- Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ce sun yi wa marigayin adddu'ar samun salama tare da bai wa iyalansa haƙurin rashin da suka yi
- A nasa jawabin, Malam Nasiru El-Rufai ya yabawa Atiku bisa yadda ya jagoranci tsare-tsaren bunƙasa tattalin arziki a mulkin Obasanjo
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Delta - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar da tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai sun sake haɗuwa a wurin ta'aziyya.
Atiku da El-Rufai sun kai ziyarar ta'aziyya ga iyalan marigayi shugaban kungiyar yankin Neja Delta watau PANDEF, Cif Edwin Clark.

Asali: Facebook
Wazirin Adamawa ya bayyana hakan wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X wanda aka fi sani da Tuwita haɗe da bidiyon ta'aziyyar da suka je tare da El-Rufai.

Kara karanta wannan
Kwana ya ƙare: Gwamna ya kaɗu da tsohon sanata ya riga mu gidan gaskiya a Najeriya
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Edwin Clark, wanda ya kasance jigo a siyasar Najeriya da fafutukar kare hakkin yankin Neja Delta, ya rasu a ranar 17 ga Fabrairu, 2025 yana da shekaru 97.
Atiku da El-Rufai sun je ta'aziyya
Atiku ya bayyana cewa ya jagoranci tawaga zuwa gidan marigayin domin yi masu ta'aziyya trae da addu'ar Allah ya ba su haƙuri da salama.
“A yau, na jagoranci wata tawaga da ta hada da tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, mun kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan babban jigo a kasar nan, Cif Edwin Clark."
“Na tunatar da iyalan cewa rasuwarsa ba su kadai ta shafa ba, rashi ne babba ga kungiyar PANDEF, yankin Neja Delta, da Najeriya baki ɗaya," in ji Atiku.
Atiku ya ƙara da cewa hanya mafi dacewa da za a girmama Edwin Clark ita ce shugabanni su jajirce wajen haɗa kan al'umma da adalci a Najeriya.
A cewarsa, wadannan sune abubuwan da marigayin ya tsaya a kai har zuwa karshen rayuwarsa.

Asali: Twitter
Malam El-Rufai ya yabawa Atiku
A yayin ziyarar, Nasir El-Rufai ya yaba wa Atiku Abubakar bisa rawar da ya taka wajen bunkasa tattalin arzikin Najeriya lokacin da yake mataimakin shugaban kasa a gwamnatin Olusegun Obasanjo.
Tsohon gwamnan ya ce ba a cika faɗar alherin da Atiku ya yi wa Najeriya ba a lokacin da yake kan mulki.
“Ba a cika fitowa ana yaba masa ba dangane da yadda ya jagoranci shirye-shiryen bunkasa tattalin arziki a lokacin mulkin Obasanjo ba.
"Da dama daga cikin ci gaban da aka samu a wancan lokacin sun gudana ne bisa jagorancinsa.”
A karshen ziyarar, tawagar ta yi addu’a don marigayin tare da yi wa iyalan da ya bari fatan alheri.
Osun: Atiku ya soki Gwamnatin Tinubu
A wani labarin, kun ji cewa Atiku Abubakar ya caccakin gwamnatin tarayya karkashin Bola Ahmed Tinubu da yinkuririn yin karfa-ƙarfa a jihar Osun.
Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasar ya ce bai kamata a tilasta wa mutanen Osun abin da ba su so ba, inda ya nemi APC ta daina siyasar tayar da zaune tsaye.
Asali: Legit.ng