Tsadar Rayuwa: Kasashen Afirika 5 Masu Fama da Matsalar Yunwa

Tsadar Rayuwa: Kasashen Afirika 5 Masu Fama da Matsalar Yunwa

Yunwa da rashin wadatar abinci suna daga cikin matsalolin da suka addabi kasashe da dama a nahiyar Afirka.

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Waɗannan kalubale sun samo asali ne daga rikice-rikice, canjin yanayi, taɓarɓarewar tattalin arziƙi, da rashin noma.

Kasashen Afirika masu fama da yunwa
Kasashen da ke fama da yunwa a Afirika Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Kasashen Afirika masu fama da yunwa

Bayanan da aka samo daga ƙididdigar Global Hunger Index - GHI na shekarar 2024 sun nuna cewa ƙasashe da dama a Afirka suna fama da matsananciyar yunwa da rashin wadatar abinci mai gina jiki.

Ga jerin wasu daga cikin ƙasashen a nan ƙasa:

1. Somaliya

Somaliya ita ce ƙasar da ta fi fama da matsalar yunwa a nahiyar Afirika.

Tana fama da matsalar rikice-rikice waɗanda suka ɗauki dogon lokaci ana yi, matsalar fari da ambaliyar ruwa.

Rikice-rikicen da ke faruwa a Somaliya suna katse ayyukan noma da rarraba abinci.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta ɓullo da sabon tsari, za ta riƙa biyan mutane kudi don su halarci makarantu 2

Fari na yawan lalata gonaki da kashe dabbobi, wanda hakan yake sanya miliyoyin mutane cikin halin ni-ƴa-su.

Kusan rabin al’ummar Somaliya na dogara ne da agajin abinci don biyan buƙatunsu na yau da kullum.

2. Chadi

Ƙasar Chadi da ke makwabtaka da Najeriya ita ce ƙasa ta biyu da matsalar yunwa ta fi ƙamari a nahiyar Afirika.

Ruwan sama mara tabbas da kwararowar hamada sun rage yawan amfanin gona a Chadi.

Rikice-rikice a ƙasashe makwabta sun tilastawa mutane gudun hijira zuwa Chadi, wanda hakan ya ƙara matsin lamba ga albarkatun ƙasar.

Rashin ingantattun hanyoyin sufuri, tare da lalacewar hanyoyi, ya sanya kai abinci da kayan agaji ga masu buƙata ya yi wahala.

Kusan mutane miliyan 4.7 a Chadi na fama da matsalar yunwa.

3. Madagascar

Madagascar tana fama da matsanancin rashin abinci wanda canjin yanayi ke haddasawa.

Fari da guguwar (cyclone) sun lalata gonakin da ake nomawa musamman a yankunan Kudancin ƙasar.

Yankin Kudu na ƙasar Madagascar yana fuskantar mafi munin fari cikin shekaru masu yawa.

Kara karanta wannan

Ma'aikatan lafiya za su kawo cikas a Katsina, sun yi gargadi

Talauci yana hana mutane farfaɗowa daga asarar amfanin gona ko samun damar siyan abinci.

Kusan rabin yara a Madagascar na fama da rashin wadatar abinci mai gina jiki, wanda hakan ke hana ci gabansu.

Sama da mutane miliyan 1.5 sun fuskanci matsalar yunwa a Madagascar a shekarar 2024.

4. Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo (DRC)

Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo (DRC) na ɗaya daga cikin ƙasashen da ke fama da matsalolin yunwa a duniya.

Hakan ya samo asali ne sakamakon rikice-rikice, talauci, da rashin tsarin aikin noma mai kyau.

Tashe-tashen hankula a yankin gabashin DRC sun tilastawa miliyoyin mutane barin gidajensu, wanda hakan ya kawo cikas ga ayyukan noma da samar da abinci.

Taɓarɓarewar tattalin arziƙi, wanda ya haɗa da hauhawar farashi da rashin ayyukan yi, ya sa abinci ya gagara ga yawancin jama'a.

Duk da kasancewar DRC tana da ƙasar noma, aikin gona bai ci gaba saboda rashin zuba hannun jari. Mutane kusan miliyan 26.4 na fama da yunwa a ƙasar, rahoton africacenter.org ya tabbatar.

Kara karanta wannan

"A bar mu da talaucinmu": Shettima ya fadi matsayarsa kan dogara da tallafin turawa

5. Nijar

Nijar tana fuskantar matsananciyar yunwa saboda yawan ƙaruwar al’umma, rashin tsayayyen shugabanci, da matsalolin yanayi.

Ƙaruwar yawan jama'a cikin sauri yana haifar da ƙaruwar bukatar abinci, amma akwai ƙarancin albarkatu a ƙasar.

Rashin isashshen ruwan sama da kwararowar hamada sun rage yawan amfanin gonan da ake samu, cewar rahoton wfp.org

Rikice-rikicen na masu ɗauke da makamai a kan iyakokinta sun tilastawa mutane barin gidajensu, wanda hakan ya kawo naƙasu ga ayyukan noma.

Fiye da mutane miliyan 4.3 a Nijar sun fuskanci barazanar yunwa a shekarar 2024.

Ƴar majalisa a Najeriya na fama da yunwa

A wani labarin kuma, kun ji cewa wata ƴar majalisar wakilai a Najeriya ta bayyana cewa tana fama da yunwa kamar sauran mutanen ƙasar.

Honorabul Adewunmi Onanuga ta buƙaci ƴan Najeriya da su rungumi harkar noma hannu bibbiyu, domin yaƙi da matsalar yunwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng