Babban Lauya Ya Bukaci INEC Ta Daina Yin Zaben Cike Gurbi, Ya ba da Mafita
- Femi Falana ya yi magana kan zaɓukan cike gurbi da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) take gudanarwa a ƙasar nan
- Babban lauya ya bayyana cewa zaɓukan cike gurbin basu da wani amfani face haifar da asarar kuɗi
- Femi Falana ya buƙaci hukumar INEC ta daina gudanar da zaɓukan idan wani ɗan takara ya rasu ko ya yi murabus daga kan muƙaminsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Lauyan kare haƙƙin ɗan adam, Femi Falana (SAN), ya ba hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) shawara.
Femi Falana ya buƙaci hukumar zaɓe Mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta daina gudanar da zaɓukan cike gurbi a ƙasar nan.

Source: Twitter
Jaridar The Punch ta rahoto Femi Falana na cewa irin waɗannan zaɓukan ba su da wani amfani face haifar da asarar kuɗi.

Kara karanta wannan
'Dan Majalisar Tarayya na Kano na tsaka mai wuya, yunƙurin tsige shi ya kara tsananta
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Femi Falana ya ba INEC shawara
Femi Falana ya bayyana cewa tun da ƙuri’un da ake samu a zaɓe na jam’iyyun siyasa ne, bai kamata a yi zaɓe ba domin maye gurbin ƴan takarar da aka zaɓa sakamakon rasuwa ko murabus ba.
"Ya kamata a umarci jam’iyyun siyasa da suka ɗauki nauyin ƴan takarar da suka mutu ko suka yi murabus, da su da cike gurbinsu ta hanyar tsayar da wani sabon ɗan takara."
“Saboda haka, majalisar tarayya ta gyara dokar zaɓe domin ba jam’iyyun siyasa damar maye gurbin jami’an gwamnati da aka zaɓa waɗanda suka rasa muƙamansu sakamakon mutuwa, murabus ko tsige su daga ofis."
- Femi Falana
Falana ya ba da misalai
Babban lauyan ya kawo misalai na shari’o’in da suka shafi wannan batu da tanadin da kundin tsarin mulki ya yi.
"Bisa tanadin sashe na 221 na kundin tsarin mulkin Najeriya, jam’iyyun siyasa ne ke lashe zaɓe ba ƴan takara ba."
"A shari’ar Amaechi vs. INEC & Ors (2008) LCN/3642 (SC), Kotun Koli ta yanke hukunci cewa sashe na 221 ya kawar da yiwuwar ƴan takara masu zaman kansu a zaɓukanmu, da kuma muhimmancin jam’iyyun siyasa."
"Idan babu jam’iyyun siyasa, ɗan takara ba zai iya tsayawa takara ba."
"A cikin gudunmawarsa ga wannan hukunci, mai Shari’a Pius Olayiwola Aderemi (wanda ya riga mu gidan gaskiya) ya bayyana cewa a lokacin zaɓe masu kaɗa ƙuri'a suna zaɓen jam’iyyun siyasa ne."
- Femi Falana
Femi Falana ya kuma kawo misalin shari'ar PDP v. INEC. (1999)7SC (PT II) 30, inda Boni Haruna ya zama gwamnan jihar Adamawa bayan murabus ɗin gwamnan da aka zaɓa, Atiku Abubakar, wanda aka tsayar a matsayin ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na PDP.
Sai dai, a cewaraa, INEC ta sauya dokar ba tare da wani dalili ba, lokacin da ta yanke shawarar gudanar da zaɓe na musamman bayan rasuwar Abubakar Audu, wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar Kogi.
Femi Falana ya faɗi Sarkin Kano
A wani labarin kuma, kun ji cewa babban lauya, Femi Falana (SAN), ya yi bayani kan hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara ta yanke kan rikicin sarautar Kano.
Babban lauyan ya dage cewa Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, shi ne sarkin Kano ɗaya tilo duk kuwa da jayayyar da wasu suke da ita.
Asali: Legit.ng
