Ministan Tinubu Zai Kashe N300m wajen Siyo Tebura da Kujerun Ofis, Ya Fadi Dalili

Ministan Tinubu Zai Kashe N300m wajen Siyo Tebura da Kujerun Ofis, Ya Fadi Dalili

  • Ministan walwala da yaƙi da talauci ya kare matakin da ya dauka na sanya N300m da ma'aikatarsa ta yi domin siyo kayan ofis
  • Nentawe Goshwe Yilwatda ya bayyana cewa ma'aikatar na buƙatar kuɗaɗen ne domin akwai gyare-gyare da take son aiwatarwa
  • Ministan ya bayyana cewa jama'a ne za su amfana da fiye da kaso 99% na kasafin kuɗin N500bn da aka warewa ma'aikatar a 2025

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ministan walwala da yaƙi da talauci, Nentawe Goshwe Yilwatda, ya yi magama kan shirin kashe sama da N300m wajen siyo kayan ofis a ma'aikatarsa.

Nentawe Yilwatda ya kare shirin ma'aikatarsa na kashe sama da N300m domin siyo kayayyakin amfani a ofis a kasafin kuɗin 2025.

Minista jinkai zai kashe N300m
Nentawe Yilwatda ya ce ma'aikatar na bukatar kudaden Hoto: Nentawe Goshwe Yilwatda
Asali: Twitter

Nentawe Yilwatda ya kare kasafin kuɗin ma'aikatarsa na shekarar 2025 ne yayin wata hira da aka yi da shi a shirin The Morning Show na tashar Arise TV a ranar Laraba, 15 ga watan Janairu, 2025.

Kara karanta wannan

Ana shirin ƙara farashin fetur a Najeriya, NNPCL ya tara wa gwamnati Naira tiriliyan 10

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa za a kashe N300m kan siyo kayan ofis?

Ministan ya bayyana cewa ma'aikatarsa na buƙatar kashe kuɗaɗen duk kuwa da halin yanayin da ake ciki a ƙasar nan.

Jaridar Vanguard wacce ta bibiyi hirar ta ce ya bayyana cewa sababbin hukumomin da aka ƙirƙiro a ƙarƙashin ma'aikatarsa suna buƙatar kayan ofis domin su gudanar da ayyukansu.

Ya ce hukumomin ba su da wuraren zama ko kayan ofis, inda ya ƙara da cewa kuɗaɗen da aka tanada a kasafin kuɗin 2025 don siyo kayayyakin sun haɗa da gyaran ofishinsa.

"Muna da sababbin hukumomi da aka ƙirƙiro waɗanda ba su da wuraren zama a baya, kamar NSIPA da wasu daga cikin hukumomin da muke da su."
"Ba su da ofisoshi a baya. Don haka muna ɗaukar matakan mayar da su zuwa wuraren da suka dace yayin da muke neman sababbin wuraren zama da za su koma."
"Ma’aikatata, an mayar da ita daga inda take a yanzu zuwa wani ɓangare daban a ma’aikatar sadarwa. Sabon ɓangare ne aka ba mu."

Kara karanta wannan

Saurayin da ya yanke wuyan budurwarsa 'yar NYSC ya ce bai yi nadama ba

"Za mu gyara wuraren da aka ba mu, tare da samar da kayan aiki ga NSIPA wacce sabuwar hukuma ce a ƙarƙashinmu. Wannan shi ne dalilin da ya sa dole ne mu nemi waɗannan kuɗaɗen."

- Nentawe Goshwe Yilwatda

Jama'a za su amfana da kasafin 2025

Sai dai, ministan ya tabbatar da cewa fiye da kaso 99% na kasafin kudin ma’aikatarsa za su kai ga talakawa ne kai tsaye.

Yilwatda ya bayyana cewa kasafin kudin ya tanadi sama da N500bn don manyan ayyuka kamar shirin ciyar da dalibai, raba tallafin kuɗi da bayar da tallafi ga mabuƙata.

'Talauci ya fi yawa a Arewa', Minista

A wani labarin kuma, kun ji cewa ministan walwala da yaƙi da talauci, Nentawe Yilwatda, ya yi magana kan talaucin da ake fama da shi a ƙasar nan.

Nentawe Yilwatda wanda ya yi tsokaci kan talauci a Najeriya, ya bayyana cewa fatara tafi ƙamari a tsakanin mutanen yankin Arewa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng