Kwana Ya Kare: Tsohon Sakataren Gwamnatin Jiha a Najeriya Ya Rasu

Kwana Ya Kare: Tsohon Sakataren Gwamnatin Jiha a Najeriya Ya Rasu

  • An shiga jimami a jihar Kwara bayan samun labarin rasuwar tsohon sakataren gwamnatin jihar (SSG), Alhaji Saka Abimbola Isau
  • Marigayin wanda ya taɓa riƙe muƙamin Antoni Janar kuma kwamishinan shari'a na jihar Kwara, ya rasu bayan ƴar gajeruwar jinya a ranar Asabar, 4 ga Janairu
  • Gwamnan Kwara, Alhaji Abdulrahman Abdulrazaq ya aika da saƙon ta'aziyyarsa kan rasuwar marigayin wanda ya taka rawa a fagen siyasar jihar

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kwara - Tsohon sakataren gwamnatin jihar Kwara (SSG) kuma babban lauyan Najeriya (SAN), Alhaji Saka Abimbola Isau ya rasu.

Alhaji Saka, wanda babban jigo ne a jam’iyyar PDP a jihar Kwara, ya rasu ne a wani asibiti da ba a bayyana ba a Adewole, da ke birnin Ilọrin.

Tsohon SSG na Kwara ya rasu
Alhaji Saka Abimbola Isau ya rasu a ranar Asabar Hoto: @FollowKWSG
Asali: Twitter

Tsohon SSG na Kwara ya rasu

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa marigayin ya rasu ne yana da shekara 69, a ranar Asabar bayan ya yi fama da gajeruwar rashin lafiya.

Kara karanta wannan

Ajali ya yi: Sarki a Najeriya ya gamu mummunan hatsari, Allah ya yi masa rasuwa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Alhaji Saka wanda na hannun daman tsohon shugaban majalisar dattawa, Dr Bukola Saraki ne, ya taɓa zama antoni janar kuma kwamishinan shari’a a zamanin gwamnatin Saraki.

An ce ya kasance cikin ƙoshin a ranar Juma’a lokacin da ya halarci taron kwamitin amintattu na babban masallacin Juma’a na Ilọrin.

Duk da babu cikakkun bayanai kan mutuwarsa, wani tsohon ma’aikacinsa da ya gwammace a sakaya sunansa, ya ce marigayin ya daɗe yana fama da ciwon suga da hawan jini.

Alhaji Saka Isau wanda ya shirya yin bikin cika shekara 70 a watan Maris, ya rasu ya bar matarsa ​​da ƴaƴansa huɗu, wanda ɗaya daga cikinsu lauya ne.

Yaushe za a yi jana'izar marigayin

Za a gudanar da jana'izar marigayin a ranar Lahadi a gidansa dake unguwar Gaa Aremu a birnin Ilorin.

Marigayin ya kasance wanda ya taka rawa a fagen a siyasar jihar Kwara.

A shekarar 2019, ya nemi tikitin takarar gwamna na jam’iyyar PDP, amma ya janye domin goyon bayan tsohon ɗan majalisar wakilai, Razak Atunwa.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya ziyarci IBB, ya bayyana abubuwan da suka tattauna a kan Najeriya

Labarin rasuwarsa ya girgiza jihar tare da sanya jimami, inda abokansa na siyasa suka aika da saƙonnin ta'aziyya.

Gwamnan Kwara ya yi ta'aziyya

A cikin saƙon da ya aike a daren ranar Asabar a shafin X, Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq ya mika ta’aziyya ga iyalai da ƴan uwan ​​marigayin.

Gwamna Abdulrazaq ya ce za a riƙa tunawa da marigayin kan hidimar da ya yi wa jihar a matsayinsa na tsohon SSG kuma kwamishinan shari’a.

Ya kuma roƙi Allah Maɗaukakin Sarki da ya shigar da marigayin Al-Jannah Firdaus, ya kuma ba iyalansa haƙurin jure wannan rashin da suka yi.

SSG na Ondo ya rasu

A wani labarin kuma, kun ji cewa sakataren gwamnatin jihar Ondo, Temitaye Oluwatuyi Oluseye, ya yi bankwana da duniya, bayan ya gamu da hatsarin mota.

Rahotanni sun bayyana cewa marigayin ya yi hatsarin motan ne a ranar, 15 ga watan Disamban 2024, sannan ya rasu a ranar Asabar 4 ga watan Janairun 2025 sakamakon raunukan da ya samu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng