Ana Batun Tsadar Mai, Gwamnatin Sokoto Ta Samar da Shirin Saukaka Zirga Zirga

Ana Batun Tsadar Mai, Gwamnatin Sokoto Ta Samar da Shirin Saukaka Zirga Zirga

  • Gwamnatin jihar Sokoto ƙarƙashin jagorancin Gwamna Ahmed Aliyu ta rangwanta kan samar da ababen hawa ga ƴan Achaɓa
  • Gwamna Ahmed Aliyu ya ƙaddamar da rabon keke Napep da babura guda 1500 a kan ragin kaso 80% cikin 100%
  • Ya bayyana cewa an ba da ababen hawan ne bisa farashi mai rahusa domin saukaka zirga-zrigar mutane a jihar

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Sokoto - Gwamnatin jihar Sokoto ta raba babura 1,000 da keke Napep guda 500 ga ƴan Achaɓa bisa farashi mai rahusa.

Gwamnatin ƙarƙashin jagorancin Gwamna Ahmed Aliyu ta raba ababen hawan ne akan rangwamen kaso 80% cikin kaso 100%

Gwamnatin Sokoto ta raba babura
Gwamnatin Sokoto ta raba babura kan farashi mai rahusa Hoto: @honnaseerbazzah
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Gwamna Ahmed Aliyu, ya ƙaddamar da rabon ababen hawan a ranar Asabar, 4 ga watan Janairun 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa gwamnatin Sokoto ta sauƙaƙa?

Kara karanta wannan

Fadan Fulani da makiyaya ya barke a Jigawa, an samu asarar rayuka

Gwamna Ahmed Aliyu ya ce an yi hakan ne domin sauƙaƙa zirga-zirga a cikin manyan biranen jihar da ƙananan hukumomin jihar ga talakawa.

Ya ƙara da cewa hakan na daga cikin matakai da dama da aka ɗauka na samar da ƙarin ayyukan yi a jihar, tare da kyautata rayuwar waɗanda suka amfana da iyalansu.

A cewarsa, an sayi keke Napep ɗin kan kudi N3.6m, sannan kuma an sayi baburan kan N1.3m, amma an raba su a kan farashi mai rahusa.

"Muna ba da keke Napep a kan N1m da babur a kan N300,000 bayan an biya kuɗin farko na N150,000 na keke Napep da N50,000 na babur tare da mutum ɗaya da zai tsayawa kowane mai cin gajiyar shirin."
"Ana sa ran waɗanda suka ci gajiyar shirin za su rika biyan N15,000 (na keke Napep) da kuma N5000 (na babur) a kowane wata."

- Gwamna Ahmed Aliyu

A yayin da ya buƙaci waɗanda suka ci gajiyar tallafin da su rangwantawa fasinjojinsu ta hanyar rage farashi, ya gargaɗe su da karya ƙa’idojin yarjejeniyar.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya ɗebo ruwan dafa kansa da ya taɓa ƙimar Atiku, matasa sun masa rubdugu

Abin a yaba ne

Wani mazaunin birnin Sokoto, Nura Garba, ya shaidawa Legit Hausa cewa abin da gwamnan ya yi, abin a yaba ne.

Ya nuna cewa hakan zai sanya mutane masu ɗan ƙaramin ƙarfi da ba su da isashshen jari, su samu abin da za su riƙa neman na abinci.

"Eh wannan abin a yaba kuma an sauƙaƙawa mutane. Ba da kayayyakin a kan farashi mai rahusa zai taimaka sosai wajen samar da abin yi ga jama'a."

- Nura Garba

Gwamnan Sokoto ya rantsar da kwamishinoni

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu, ya rantsar da sababbin kwamishinoni da za su yi aiki a majalisar zartaswar jihar.

Gwamnan ya rantsar da kwamishinoni bakwai, masu ba da shawara takwas da manyan sakatarori tara, bayan wasu daga cikinsu sun yi murabus domin yin takara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng