Kamfanonin Sadarwa a Najeriya na Son Kara Farashin Kira da Kashi 100

Kamfanonin Sadarwa a Najeriya na Son Kara Farashin Kira da Kashi 100

  • Kamfanonin sadarwa a Najeriya sun bayyana bukatar gwamnatin Najeriya ta amince da bukatar da suka gabatar mata
  • Shugaban kamfanin MTN Najeriya, Karl Toriola ya bayyana cewa sun mika bukatar a amince da su kara farashin kiran waya
  • Sun shaida cewa dole ne ta sa suka nemi gwamnati ta amince da su yi karin biyo bayan hauhawar farashi da ake fama da shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Kamfanonin sadarwa na Najeriya sun mika bukatarsu gwa gwamnatin kasar na karin kudin kiran waya da 100%.

Kamfanonin sun bayyana cewa tuni aka mika wannan bukata ga Hukumar sadarwa ta kasa (NCC) domin samun sahalewar gwamanti.

Kevin Carter
Kamfanonin sadarwa za su kara kudin kiran waya Hoto: Kevin Carter/MTN Nigeria
Asali: Getty Images

Jaridar Punch ta wallafa cewa kamfanonin sadarwa sun jaddada bukatar a amince masu da yin karin ne saboda yadda hauhawar farashi ya addabe su.

Kara karanta wannan

"An shiga wahala bayan zaben Tinubu," Sanatan APC ya fadi manufar gwamnati

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamfanonin sadarwa za su kara kudin kira

Arise TV ta wallafa cewa Shugaban kamfanin MTN Najeriya, Karl Toriola, ya ce za su kara kudin kiran waya da 100% da zarar NCC ta ba su damar yin hakan.

A cewarsa, bukatar karin kudaden wajen tabbatar da dorewar masana’antar, wadda ke fama da matsin lamba na kudi saboda karuwar kudaden gudanarwa.

Kamfanonin sadarwa ba su da kwarin gwiwa

Shugaban kamfanin MTN Najeriya, Karl Toriola, Toriola ya ce ba su da tabbacin cewa gwamnatin tarayya za ta amince da karin kudin kira da suka bukata.

Idan NCC ta amince da bukatar, wannan na nufin jama’a za su rika biyan N20 a kiran wayan da suke biyan N10 a baya.

Ba wannan ne karon farko da kamfanonin suka nemi karin farashin kira ba, an taba neman karin a watan Afrilu 2024.

NCC ta kai kamfanin sadarwa zuwa kotu

A wani labarin, kun ji yadda NCC ta garzaya gaban kotu inda ta shigar da karar kamfanin sadarwa na MTN da wasu mutum uku bisa zargin keta hakkin mallaka.

Kara karanta wannan

Kamfanonin sadarwa na yunkurin kara kudin kira, data da sako, sun bayyana dalilai

NCC ta na tuhumar kamfanin da amfani da wakar wani mawaki, Maleke Idowu Moye ba tare da an nemi izininsa ba, wanda ta ce ya saba da dokar mallaka ta Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.