Tsoron Bincike Ya Sa SSG Yin Murabus a Bauchi? An Gano Gaskiya

Tsoron Bincike Ya Sa SSG Yin Murabus a Bauchi? An Gano Gaskiya

  • Jita-jita ta riƙa yawo kan cewa tsohon sakataren gwamnatin jihar Bauchi (SSG), ya yi murabus ne saboda tsoron a bincike shi
  • Barista Ibrahim Muhammad Kashim ya fito ya bayyana cewa ko kaɗan tsoron a bincike shi, ba shi ba ne dalilinsa na ajiye muƙamansa
  • Ya bayyana jita-jitar da ake yaɗawa a kansa a matsayin abin dariya wanda baya da tushe ballantana makama

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Bauchi - Tsohon sakataren gwamnatin jihar Bauchi, Barista Ibrahim Muhammad Kashim, ya yi magana kan murabus ɗin da ya yi daga kan muƙaminsa.

Ibrahim Muhammad Kashin ya yi watsi da jita-jitar da ake yadawa cewa ya yi murabus daga muƙaminsa na SSG, domin gudun ka da hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta jihar ta tuhume shi.

Tsohon SSG na Bauchi ya fadi dalilin murabus
Tsohon SSG na Bauchi baya tsoron bincike Hoto: Sen. Bala Abdulkadir Mohammed
Asali: Facebook

Tsohon sakataren gwamnatin na jihar Bauchi ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da jaridar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Gwamna ya gargadi jami'an gwamnati kan shiga siyasa a 2025, ya fadi matakin dauka

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya yi watsi da zarge-zargen a matsayin marasa tushe, waɗanda babu gaskiya a cikinsu kuma ba su kamata ba.

Meyasa Ibrahim Kashim ya yi murabus?

Sai dai, Barista Kashim ya ce murabus ɗin nasa ba shi da alaƙa da binciken da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar ke yi kan wasu jami’an gwamnati.

"Bisa ƙashin kai na na yi murabus, domin duk abin da yake da farko yana da ƙarshe. Ba wani abu ba ne ka shiga gwamnati, daga baya ka yi murabus idan kana so."
"Domin haka, batun mutane su ce na yi murabus domin gujewa bincike, ina ganin abin dariya ne. Magana ta gaskiya babu hankali a cikin wannan zancen kwata-kwata."
"Na yi amanna cewa zai fi sauƙi ga hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta bincike ni a lokacin da nake wajen gwamnati fiye da na ina cikin gwamnati."

- Ibrahim Muhammad Kashim

Kara karanta wannan

Duk da barazanar sojoji, Bello Turji ya ci gaba da ta'addanci a Zamfara

Meye alaƙar tsohon SSG da Gwamna Bala?

Da aka tambaye shi game da dangantakarsa da Gwamna Bala Mohammed, tsohon SSG ya ce har yanzu suna da alaƙa mai kyau a tsakaninsu.

"A sani na babu wata ƴar tsama a tsakani na da gwamma. A lokacin da na yi niyyar yin murabus na tattauna da gwamna kuma ya ba ni damar yin murabus."
"Zan iya fada muku cewa duk waɗannan abubuwan da ake fada game da murabus ɗina ba komai ba ne illa suratai ne kawai."

- Ibrahim Muhammad Kashim

Gwamnan Bauchi ya naɗa sabon SSG

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed ya naɗa sabon sakataren gwamnati bayan murabus ɗin Barista Ibrahim Muhammad Kashim.

Gwamna Bala Mohammed ya naɗa Aminu Hammayo a matsayin wanda zai riƙe muƙamin sakataren gwamnatin jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng