Obasanjo Ya Gano Wadanda Suka Jefa Najeriya cikin Matsala

Obasanjo Ya Gano Wadanda Suka Jefa Najeriya cikin Matsala

  • Tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya nuna damuwarsa kan tarin ƙalubale da matsalolin da Najeriya ke fuskanta
  • Olusegun Obasanjo ya ɗora alhakin matsalolin da suka addabi ƙasar nan a kan shugabanni da kuma mabiyansu
  • Tsohon shugaban ƙasan ya buƙaci ƴan Najeriya da ka da gwiwoyinsu su sare wajen fatan ganin cewa al'amura sun gyaru a ƙasar nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Ogun - Tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya yi magana kan ƙalubale da tarin matsalolin da Najeriya ke fuskanta.

Olusegun Obasanjo ya ɗora alhakin matsalolin da Najeriya ke fuskanta a halin yanzu kan ayyukan shugabanninta da kuma gudunmawar mabiyansu.

Obasanjo ya fadi matsalolin Najeriya
Obasanjo ya koka kan halin da Najeriya take ciki Hoto: Sen. Bala Abdulkadir Mohammed
Asali: Facebook

Tsohon shugaban ƙasan ya bayyana hakan ne yayin wata tattauna da tashar Arise tv a ranar Litinin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Obasanjo ya ƙarfafa gwiwar ƴan Najeriya

Duk da wahalhalun da ake fuskanta, Obasanjo ya buƙaci ƴan Najeriya da su kasance masu fatan alheri, ka da su yanke ƙauna wajen gyaruwar al'amura yayin da ake shirin shiga sabuwar shekara.

Kara karanta wannan

Sojoji sun fafata da 'yan bindiga, an rasa rayukan jami'an tsaro

Tsohon shugaban ƙasan ya nuna ƙwarin gwiwar cewa nan ba da daɗewa ba Najeriya za ta koma matsayin da ya dace da ita a cikin ƙasashe, yana mai jaddada cewa ya kasance mai kyakykyawan fata game da makomar ƙasar.

"Inda mu ke a yanzu ba nan Allah yake son ganinmu ba, kuma na yi amanna cewa nan kusa ko zuwa nan gaba za mu je inda Allah yake so ya ganmu."
"Allah yana son Najeriya ta kasance mai cike da ni'ima da wadata, ba ƙasa wacce ta gaza ba."
"Inda muka tsinci kanmu a yanzu ya faru ne sakamakon ayyukan shugabanninmu da mabiyansu, amma Allah, Allah ne kuma yana da shiri mai kyau a kan Najeriya."
"Na yi amanna cewa Allah yana da tanadi mai kyau a kan Najeriya a nan gaba."

- Olusegun Obasanjo

Tsohon hadimin Buhari ya caccaki Obasanjo

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon hadimin shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya soki Olusegun Obasanjo wanda ya taɓa jan ragamar shugabancin Najeriya.

Kara karanta wannan

Bayan kwanaki 3 Shettima ya yi magana kan iftila'in harin bam a Sokoto

Garba Shehu ya caccaki tsohon shugaban ƙasan ne kan yadda yake maganganu marasa daɗi a kan shugabannin da suka biyo bayansa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng