Mutuwa Ta Sake Ratsa Iyalan Gwamnan Jigawa Kwana 1 bayan Rasuwar Mahaifiyarsa

Mutuwa Ta Sake Ratsa Iyalan Gwamnan Jigawa Kwana 1 bayan Rasuwar Mahaifiyarsa

  • Gwamnan jihar Jigawa, Ahmed Umar Namadi, ya sake rasa ɗaya daga cikin iyalansa a ranar Alhamis, 26 ga watan Disamban 2024
  • Yaron gwamnan mai suna Abdulwahab Umar Namadi ya rasu da yammacin ranar Alhamis sakamakon wani mummunan hatsarin mota da ya ritsa da shi
  • Rasuwarsa na zuwa ne kwana ɗaya bayan mahaifiyar Gwamna Umar Namadinta riga mu gidan gaskiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Jigawa - Allah ya yi wa yaron gwamnan jihar Jigawa, Ahmed Umar Namadi rasuwa.

Yaron na Gwamna Namadi mai suna AbdulWahab Umar Namadi ya rasu ne a ranar Alhamis, 26 ga watan Disamban 2024.

Yaron gwamnan Jigawa ya rasu
Yaron gwamnan Jigawa ya rasu Hoto: @uanamadi
Asali: Twitter

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun sakataren yaɗa labaran gwamnan, Hamisu Mohammed Gumel wacce aka sanya a shafin X na Gwamna Ahmed Umar Namadi.

Kara karanta wannan

"Mun rasa uwa ta gari," Abba Kabir ya ce bayan rasuwar mahaifiyar gwamna

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yaron Gwamna Namadi ya rasu

Sanarwar ta bayyana cewa Abdulwahab ya rasa ransa ne sakamakon wani hatsarin mota da ya ritsa da shi a kan titin Dutse zuwa Kafin Hausa da yammacin ranar Alhamis.

Rasuwar Abdulwahab Umar Namadi na zuwa ne kwana ɗaya bayan mahaifiyar Gwamna Namadi ta riga mu gidan gaskiya, a ranar Laraba, 25 ga watan Disamban 2024.

"Mai girma gwamnan jihar Jigawa, Gwamna Mallam Umar Namadi, na sanar da rasuwar wani daga cikin iyalansa, ɗansa Abdulwahab Umar Namadi."
"Ya bar duniya ne da yammacin yau (Alhamis, 26 ga watan Disamba, 2024) sakamakon wani mummunan hatsarin mota da ya auku a kan titin Dutse-Kafin-Hausa."
"Ana gudanar da jana'izarsa a wannan lokacin a garin Kafin Hausa, kamar yadda addinin Musulunci ya tanada."
"Marigayi Abdulwahab ɗan shekara 24 ya rasu ya bar iyayensa da ƴan uwansa da dama."

- Hamisu Mohammed Gumel

Tinubu ya yi wa Gwamna Namadi ta'aziyya

Kara karanta wannan

Tinubu ya mika sako ga gwamnan Jigawa, ya yi ta'aziyyar rasuwar mahaifiyar Namadi

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya miƙa saƙon ta'aziyyarsa ga Gwamna Ahmed Umar Namadi na jihar Jigawa.

Shugaba Bola Tinubu ya yi ta'aziyyar ne ga Gwamna Namadi sakamakon rasuwar mahaifiyarsa, Hajiya Maryam Namadi, wacce ta rasu a ranar Laraba, 25 ga watan Disamban 2024.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng