Kirsimeti: Gwamna a Arewa Ya Zarce Gwamnatin Tarayya, Ya ba Ma'aikata Hutun Mako 2
- Ma'aikata a jihar Benue za su kwashe makonni biyu suna yin hutu domin bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara
- Gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia ya sanar da ba da hutun ga ma'aikatan gwamnati a ranar Talata, 24 ga watan Disamban 2024
- Hyacinth Alia ya buƙaci ma'aikatan da su yi amfani da hutun wajen maida hankali kan harkokin noma domin samun wadataccen abinci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Benue - Gwamnan Benue, Hyacinth Alia ya bayar da hutun mako biyu ga ma’aikatan gwamnati a jihar.
Mai girma Gwamna Hyacinth Alia ya ba da hutun ne domin bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara.
Gwamna Alia ya ba da hutun Kirsimeti
Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin ganawa da manema labarai a gidan gwamnati da ke Makurdi, cewar rahoton jaridar Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan ya kuma ƙarfafa gwiwar ma’aikata da su yi amfani da hutun wajen gudanar da ayyukan noma domin bunƙasa samar da abinci, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.
Gwamna Hyacinth Alia ya ce za a fara hutun ne a ranar 24 ga watan Disamba kuma zai kare ranar 6 ga watan Janairun 2025.
Meyasa Gwamna Alia ya ba da hutu mai tsawo?
A cewar gwamnan, manufar tsawaita hutun shi ne domin ba ma’aikata a jihar damar jin daɗin bukukuwan tare da ƴan uwansu da kuma amfani da lokacin wajen ayyukan noma domin inganta samar da abinci a jihar.
"Ina kira gare ku da ku yi amfani da wannan dogon hutun domin mayar da hankali kan harkokin noma domin tabbatar da wadatar abinci a jihar."
- Gwamna Hyacinth Alia.
Gwamnan ya bayyana cewa an cire masu muhimman ayyuka kamar bankuna da hukumomin tsaro daga hutun.
Gwamnatin tarayya ta ba da hutu
A baya, rahoto ya zo cewa gwamnatin tarayya ta ba da hutu domin bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekarar 2025 da ke tafe.
Ministan harkokin cikin gida Olabunji Tunji-Ojo wanda ya sanar da ba da hutun a madadin gwamnatin tarayya, ya yi wa ƴan Najeriya murnar zuwan lokacin Kirsimeti.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng