"Gwamnatin Tinubu Ta Gaza," Jigon APC Ya Amince Sun ba Ƴan Najeriya Kunya
- Jigon APC, Jesutega Onokpasa ya bayyana cewa gwamnatin Bola Tinubu ta gaza wajen samar da wadataccen abinci ga ƴan Najeriya
- Onokpasa ya ce lokacin yakin neman zaɓe, jama'a sun rika kwatanta su da waɗanda za su share masu hawaye game da yunwar da ake fama da ita
- Sai dai a cewarsa, gwamnatin Tinubu ta gaza cika wannan alƙawari kuma hakan shi ne tushen abubuwan da ke faruwa a wurin rabon tallafi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Wani jigo a jam’iyyar APC, Jesutega Onokpasa ya ce gwamnatin tarayya karkashin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta gaza wajen samar da abinci.
Sama da mutane 30 ne suka mutu yayin da wasu da dama suka jikkata a turmutsutsun karɓar tallafin abinci a jihar Anambra da Abuja.

Source: Facebook
Da yake tsokaci kan lamarin, Onokpasa, wanda ɗan a-mutun Shugaba Bola Tinubu ne, ya yi ikirarin cewa gwamnatin tarayya ta gaza wajen samar da abinci.

Kara karanta wannan
Gwamnan PDP ya ziyarci Tinubu a Legas, an ji abin da suka tattauna a cikin bidiyo
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnatin Tinubu ta gaza a fannin abinci
Jigon APC ya faɗi haka ne a cikin shirin Sinrise Daily na gidan talabijin na Channels tv ranar Talata, 24 ga watan Disamba, 2024.
“Ina ganin tushen matsalar ita ce mu (APC) mun gaza wajen samar da isasshen abinci ga ‘yan kasa.
"A lokacin da muke yi wa wannan gwamnati kamfe, jama’a suna kiranmu da ‘Agbadoriya’ saboda kullum shugabanmu (Tinubu) yana maganar samar da abinci.
"Amma abin takaice ga shi ba mu iya samar da wadataccen abinci, dole ne mu yarda laifin mu ne," in ji Onokpasa.
Jigon APC ya ce an yi watsi da ɓangaren noma
Mista Onokpasa ya kara da cewa babu wani abin a zo a gani da gwamnatin Tinubu ta yi na bunkasa harkokin noma, wanda kuma ba wani babban abin wahala ba ne.
A cewarsa, ƴan Najeriya sun fi bukatar samun abin da za su ci fiye da rage farashin litar man fetur.

Kara karanta wannan
Babban malami a Arewa ya dura kan gwamnati, ya ce ita ta jawo rasa rayuka a jihohi 3
Wani magidanci, Malam Bala Ahmad ya shaidawa Legit Hausa cewa ba abin da za su ce kan halin ƙuncin da wannan gwamnatin ta jefa mutane sai 'Allah ya isa'.
Magidancin wanda ya ɗauki zafi ya ce duk wanda ya zaɓi APC a 2023 yana daga cikin waɗanda suka ɗauki alhakin mutane kuma sai Allah ya saka masu.
'Wallahi ana cikin mawuyacin hali, kuma abin mamakin shugaban ƙasa ya dage kan matakan da ya ɗauka. Bakomai akwai ranar Hisabi.
"Fatan da muke Allah ya kawo mana sauƙi ya kuma shirya mana shugabannin mu," in ji Bala.
Bola Tinubu ba zai kayyade farashin kaya ba
A wani rahoton, mun kawo maku cewa shugaba Bola Tinubu ya ce bai yarda da batun gwamnati ta tsoma kanta a batun farashin kayayyaki ba.
Shugaban kasar ya ce ba zai kayyade farashin kayayyakin da ake amfani da su yau da kullum ba amma zai yi duk mai yiwuwa wajen rage tsadar kayan.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng