Adesina: 'Babban Dalilin da Ya Sa Buhari Ya Ƙi Cire Tallafin Man Fetur a Mulkinsa'
- Femi Adesina ya bayyana abin da ya hana tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari cire tallafin man fetur a lokacin mulkinsa
- Tsohon kakakin shugaban ƙasar ya ce Buhari ya ƙi yarda a cire tallafi ne saboda gudun halin ƙuncin da talakawa za su shiga
- Adesina ya ce Buhari mutumin kirki ne wanda ko a lokacinsa yana taka tsan-tsan da ɗaukar matakan da za su ƙuntatawa talaka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Tsohon kakakin shugaban kasa, Femi Adesina ya ce Muhammadu Buhari ya ki yarda a tuge tallafin man fetur ne saboda gudun ƙuntatawa talakawa.
Adesina ya bayyana haka ne a sakon taya murnar cika shekaru 82 da ya turawa tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.
Yadda Muhammadu Buhari ya damu da talakawa
Kamar yadda Daily Trust, Femi Adesina ya ayyana Buhari a matsayin abokin talaka, wanda ya rika yin taka-tsan-tsan da matakin da zai ɗauka a mulkinsa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya kira Buhari da ‘Ore Mekunu’, kalmar Yarbawa da ke nufin abokin talakawa, inda ya kara da cewa har yanzu mutane na tare da tsohon shugaban duk da ba ya mulki.
Adesina ya ce Muhammadu Buhari ya kaucewa duk matakan da za su kara jefa talaka cikin talauci ko da kuwa ya san wasu gurbatattun shugabanni na amfana.
Dalilin da ya hana Buhari cire tallafi
"Babbar giwar ita ce cire tallafin man fetur, shin kuna tsammanin gwamnatin Buhari ba ta san ta nan kuɗaɗe ke dulmiyewa ba? Ta san komai.
"Amma kun san waye ya hana cire tallafin? Buhari, dalilinsa shi ne wane hali talaka zai shiga idan aka cire, damuwarsa ƴan Najeriya kada a ƙara ƙuntata masu."
"Yana gudun duk wani abu da zai jefa al’umma cikin kunci ba don komai ba kuma sai don kare mutuncin talakawa."
- Femi Adesina.
Bola Tinubu ya taya Buhari murna
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya aika sakon taya murna ga magabacinsa, Muhammadu Buhari da ya cika shekara 82.
Mai girma Bola Tinubu ya yabawa tsohon shugaban ƙasar, inda ya yi alkawarin ɗorawa daga ayyukan alherin da ya yi a Najeriya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng