Yadda Hukumar EFCC Ta Kwato N248bn, $105m a Hannun Barayi

Yadda Hukumar EFCC Ta Kwato N248bn, $105m a Hannun Barayi

  • Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC ta samu nasarori a yaƙin da take yi da masu wawushe dukiyoyin jama'a
  • Ofishin mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro (ONSA) ya bayyana cewa EFCC ta ƙwato biliyoyin Naira daga hannun ɓarayi
  • Daraktan ɓangaren shari'a na ONSA ya ce EFCC ta kuma samu nasarori a ƙararrakin da ta shigar da waɗanda ake tuhuma da laifuffuka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ofishin mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro (ONSA) ya bayyana nasarorin da hukumar yaƙi da rashawa ta EFCC ta samu.

Ofishin na NSA ya bayyana cewa hukumar EFCC ta ƙwato sama da Naira biliyan 248, Dala miliyan 105 da kuma gidaje 753.

EFCC ta kwato kudade
Hukumar EFCC ta kwato N248bn Hoto: Economic Crimes and Financial Commission
Asali: Facebook

Hukumar EFCC ta samu nasarori

Daraktan ɓangaren shari’a a ofishin ONSA, Zakari Mijinyawa ne ya bayyana hakan a yayin taron kwamitin tsare-tsare na harkokin sadarwa tsakanin hukumomin gwamnati, ranar Litinin a Abuja, cewar rahoton jaridar Vanguard.

Kara karanta wannan

"Ka watsar da su": Gwamnan PDP ya ba Shugaba Tinubu shawara

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kuma ƙara da cewa ya zuwa watan Oktoban 2024, EFCC ta samu nasara a shari'o'i 3,455.

Ya zuwa yanzu dai tsofaffin gwamnoni huɗu, tsofaffin ministoci uku, da kuma wani tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), suna fuskantar shari’a bisa zargin karkatar da kuɗaɗe da sauran laifuffuka.

An taso ɓarayin mai a gaba

A yaƙin da ake yi da satar mai, Mijinyawa ya bayyana cewa, sojoji sun daƙile satar man da ya kai na sama da Naira biliyan 57.05, rahoton jaridar Tribune ya tabbatar.

Mijinyawa ya jaddada ƙoƙarin da sojoji ke ci gaba da yi domin tabbatar da kare albarkatun man fetur na ƙasar nan.

Ya ce sojojin suna gudanar da ayyuka na musamman da nufin kawar da haramtattun wuraren tace mai da inda ake satarsa.

Tsohon gwamna ya cika baki kan EFCC

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa ya samu bakin magana bayan ya amsa gayyatar EFCC kan badaƙalar N1.3trn.

Kara karanta wannan

Shugaban INEC Mahmood Yakubu ya rasu? An gano abin da ya faru

Okowa wanda ya yi wa Atiku Abubakar mataimaki a takarar zaɓen shugaban ƙasa na 2023, ya bayyana cewa ko kaɗan bai da wata fargaba idan hukumar za ta bincike shi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng