Shugaba Tinubu Ya Jagoranci Taron FEC Babu Shettima, An Samu Bayanai
- Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya shiga taron majalisar zartaswa ta tarayya (FEC) a fadarsa da ke birnin tarayya Abuja
- Tinubu na jagorantar taron ne wanda ya samu halartar manyan ƙusoshin gwamnati da ministoci a fadar shugaban ƙasa
- Taron bai samu halartar mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ba wanda ya je ƙasar Saudiyya domin yin aikin Umrah
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Shugaba Bola Ahmed Tinubu na jagorantar taron majalisar zartarwa ta tarayya (FEC).
Mai girma Bola Tinubu yana jagorantar taron ne a fadar shugaban ƙasa da ke birnin tarayyya Abuja.
Tinubu ya jagoranci taron majalisar zartaswa
Jaridar Daily Trust ta ce taron wanda ake sa ran zai kasance na ƙarshe a shekarar 2024, yana zuwa ne gabanin gabatar da kudirin kasafin kudin shekarar 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jaridar The Nation ta rahoto cewa taron ya samu halartar sakataren gwamnatin tarayya, Sanata George Akume.
Sauran mahalarta taron sun haɗa shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila, shugabar ma'aikatan gwamnatin tarayya, Didi Walson-Jack da mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Mallam Nuhu Ribadu.
Haka kuma daga cikin mahalarta taron akwai mambobin majalisar zartaswa da suka haɗa da manyan ministoci da ƙananan ministoci.
Shettima bai halarci taron majalisar FEC ba
Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, wanda yanzu haka yake ƙasar Saudiyya domin gudanar da Umrah, bai halarci taron ba.
Ministan harkokin wajen ƙasashen waje, Ambasada Yusuf Tuggar da ƙaramar ministar harkokin ƙasashen waje, Bianca Odumegwu-Ojukwu, ba su halarci taron ba.
Karanta wasu labaran kan Tinubu
- Magana ta kare, Kotun Koli ta yi hukuncin karshe kan shari'ar neman tsige Tinubu
- Gwamnatin Tinubu za ta wuce gona da iri, bashin da aka karbo ya haura iyaka da N4trn
- Tinubu ya shiga matsala da ake zargin an handame N57bn a ma'aikata, ana tuhumarsa
Shekarau ya ba shugaba Tinubu shawara
A wani labarin kuma, kun ji cewa Malam Ibrahim Shekarau ya yi hannunka mai sanda ga gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin Bola Tinubu.
Tsohon gwamnan na jihar Kano ya buƙaci shugaban ƙasan da ya sake lale kan yadda yake jan ragamar mulkin ƴan Najeriya tun da ya shiga ofis a bara.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng