"Ina Jin Zafi": Tinubu Ya Fadi Abin da Ya Yi Wa 'Yan Najeriya ba da Son Rai ba
- Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya nuna cewa bai manta da halin matsin tattalin arziƙin da ake fama da shi a ƙasar nan
- Tinubu ya bayyana cewa ba da gangan ya ɗorawa ƴan Najeriya wahala, inda ya buƙace su da su yi haƙuri su sanya juriya
- Shugaban ƙasan ya bayyana cewa ya kawo manufofinsa ne domin yin gyara kan kura-kuran da gwamnatocin da suka gabace shi suka yi
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Osun - Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya ce yana sane da halin ƙuncin da ake ciki a ƙasar nan.
Shugaba Tinubu ya buƙaci ƴan Najeriya da su jure abin da ya bayyana a matsayin wahala wacce ba ta gangan ba.
Shugaba Tinubu ya bayyana haka ne a wajen taron yaye ɗalibai karo na 48 na jami’ar Obafemi Awolowo (OAU), da ke Ile-Ife, jihar Osun, cewar rahoton jaridar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban ƙasan ya samu wakilcin mai ba da shawara na musamman kan tattalin arziƙi, ofishin mataimakin shugaban ƙasa, Tope Fasua.
Tinubu ya ba ƴan Najeriya haƙuri?
Shugaba Tinubu ya nuna cewa ba ya jin daɗin cusawa ƴan Najeriya wahala. Ya tabbatar da cewa za a ji daɗi nan gaba.
Ya ba da tabbacin cewa manufofinsa na sake fasalin tattalin arziƙi, suna da nufin sanya Najeriya ta gyaru ta yadda kowa zai amfana da ita.
Duk da haka, ya ƙara da cewa, dole ne a jure raɗaɗin da ke tattare da manufofin na sa na ɗan lokaci.
Me Tinubu ya ce kan tsadar rayuwa?
"Ba wai ba na sane da halin matsin tattalin arziƙin da ƙasar mu take ciki ba ne, ba kuma na jin daɗin saka ƴan Najeriya cikin wahala."
"Sai dai, mun tsinci kan mu cikin wani hali sakamakon wasu manufofi da gwamnatocin baya suka ɓullo da su, waɗanda ba su samar da ci gaba ga jama'armu ba."
"Yayin da muke ƙoƙarin gyara kura-kuran da aka yi, muna kiran ƴan Najeriya da su ba mu haɗin kai, su jure wannan wahalar ta yadda a ƙarshe za mu yi murna kamar yadda masu kammala karatu suke yi a yau."
- Bola Tinubu
Gwamna ya ba Tinubu shawara
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya fito ya ba shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu shawara kan ministocinsa.
Gwamnan na jam'iyyar PDP ya bayyana cewa akwai waɗanda ya kamata a ce shugaban ƙasan ya raba gari da su a cikin gwamnatinsa.
Asali: Legit.ng