Ministan Shari'a Ya Fadi Shugabannin Kananan Hukumomin da Za a Garkame

Ministan Shari'a Ya Fadi Shugabannin Kananan Hukumomin da Za a Garkame

  • Ministan shari'a, Lateef Fagbemi ya yi magana kan ƴancin cin gashin kan da ƙananan hukumomi suka samu a ƙasar nan
  • Lateef Fagbami.ya ja kunnen shugabannin ƙananan hukumomin da su guji wawushe dukiyoyin jama'arsu
  • Ministan ya bayyana cewa duk wanda aka samu da laifin satar dukiyar jama'a, za a aika da shi zuwa gidan yari

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ministan shari'a, Lateef Fagbemi, ya ja kunnen shugabannin ƙananan hukumomi a Najeriya.

Ministan shari'an ya bayyana cewa za a gurfanar da ciyamomin da suka saci kuɗaɗen ƙananan hukumominsu.

Lateef Fagbemi ya gargadi ciyamomi
Ministan shari'a ya ja kunnen ciyamomi Hoto: @FedMinofJustice
Asali: Twitter

Lateef Fagbemi yayi magana ne a Abuja ranar Alhamis a taron shekara-shekara na ƙungiyar ƴan jarida masu aiko da rahotanni daga ɓangaren shari'a ta ƙasa (NAJUC) na 2024, cewar rahoton jaridar The Cable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Fagbemi ya gargaɗi ciyamomi

Fagbemi ya ce hukuncin da Kotun Ƙoli ta yanke kan ƴancin cin gashin kan ƙananan hukumomi, na da nufin ba su damar gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.

Kara karanta wannan

'Za a tsige ku': Gwamnatin Tinubu ta gargadi gwamnoni kan kudin kananan hukumomi

Ministan shari'an ya ce duk wani bashi da gwamnatocin jihohi suka ciyo, bai kamata a raba shi da ƙananan hukumomin ba.

Ministan ya ce yin amfani da kuɗaɗen ƙananan hukumomi ba bisa ƙa’ida ba da gwamnoni ke yi, ba daidai ba ne kuma hakan zai iya sanya a tsige gwamnan da aka samu da wannan laifin.

"Idan har su (shugabannin ƙananan hukumomi) suka zaɓi sace kuɗaɗen jama’a kuma suka kasa sauke nauyin da kundin tsarin mulki ya ba su, za su iya shiga gidan yari. Dole ne ka da su ci amanar amincewar da aka ba su.
"Dole ne kowane yaro ya samu ilmin firamare. Mata masu juna biyu da jarirai dole ne su samu ingantaccen kiwon lafiya, kuma masu rauni a cikin al'umma dole ne su ci gajiyar shirye-shiryen samar da walwala."

- Lateef Fagbemi

Ministan shari'a ya magantu kan tsadar rayuwa

A wani labarin kuma, kun ji cewa ministan shari'a na Najeriya, Lateef Fagbemi, ya yi magana kan ƙalubalen tattalin arziƙi da ake fama da shi a ƙasar nan.

Ministan ya ce duk da ƙasar nan na fuskantar ƙalubale kafin zuwan Bola Tinubu, gwamnati mai ci ba zata tsame hannunta ba kan wuyar da ake sha a ƙasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng