'Saurin Me Ake Yi?" Dattawan Arewa Sun Shawarci Gwamnati kan Kudirin Harajin Tinubu

'Saurin Me Ake Yi?" Dattawan Arewa Sun Shawarci Gwamnati kan Kudirin Harajin Tinubu

  • Kungiyar 'Arewa Consultative Forum' ta shawarci gwamnatin tarayya ta mayar da hankali a kan shawarwarin 'yan kasa kan batun haraji
  • Jami'in hulda da jama'a na kungiyar, reshen Kano, Alhaji Bello Sani Galadanchi ya bayyana cewa su na kara duba abin da kudirin ya kunsa
  • Ya shawarci gwamnatin tarayya ta tabbatar da bin dokokin dimukuradiyya, musamman a kan kudirorin da su ke da sarkakiya irinn na haraji

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Kungiyar Arewa Consultative Forum ta ce bai dace gwamnati ta rika gaggawar ingiza majalisa ta amince da kudirin haraji ba.

Jami'in hulda da jama'a na ACF, reshen Kano, Bello Sani Galadanchi ne ya shaidawa Legit haka a tattaunarmu da shi a ranar Juma'a.

Kara karanta wannan

A karo na 6, kotu ta sake ingiza keyar Mama 'Boko Haram' zuwa kurkuku

Tinubu
ACF ta shawarci gwamnati a kan kudirin haraji Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Dattijon bayyana cewa tuni ACF ta kafa kwamitin da zai kara nazarn kudirin da zummar gano sassan da ake zargin an cusa abubuwan da za su jawo matsala ga tattalin arzikin Arewa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

ACF ta shawarci gwamnatin Tinubu

Kungiyar ACF ta ci gyaran gwamnatin tarayya na cewa ba za ta janye kudirin haraji da ke gaban majalisar dattawan kasar nan ba.

"Abin da ya sa wannan kungiya ta mu ta ci gaban Arewa ta damu da wannan daftari na dokoki hudu na inganta harajin Najeriya shi ne, mu a tunaninmu, a mulkin dimukuradiyya, kullum kai me mulki kokari za ka yi ka tafi da ra'ayoyin jama'a.

Saboda haka ne ya shawarci gwamnati ta sassauta matsayarta, kuma ta tabbata ta dauki dukkanin koken jama'a, a yi gyara kafin tabbatar da kudirin.

"ACF za ta ci gaba da fafutuka," Galadanchi

Alhaji Bello Sani Galadanchi ya tabbatar da cewa kungiyar ACF ba za ta zuba idanu a kan al’amuran da za su shafi shiyyar ba.

Kara karanta wannan

Dattawan Arewa sun soki kalaman Sakataren Gwamnati kan takara da Tinubu a 2027

Ya kara da cewa batu irin na kudurin haraji ya na daga cikin abin da za su bibiya sannu a hankali, tare da bayar da shawarwarin da su ka dace ga gwamnati.

ACF ta soki maganganun sakataren gwamnati

A baya, mun ruwaito cewa kalaman sakataren gwamnatin tarayya, George Akume sun jawo ce-ce-ku-ce, ya shawarci Arewacin kasar nan ta hakura da neman takara a 2027.

Jami'in yada labaran kungiyar na kasa, Farfesa Tukur Muhammad Baba ne ya bayyana fushinsu, inda ya ce kamata ya yi a mayar da hankali a gan ci gaban Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.