Gwamna Ya Yi Alhinin Rasuwar Shugaban Karamar Hukuma, Ya Yi Wa'azi
- Mutanen ƙaramar hukumar Katcha da ke jihar Neja sun shiga jimami sakamakon rasuwar ciyaman ɗinsu a wani hatsarin mota da ya ritsa da shi
- Gwamna Mohammed Umaru Bago na jihar Neja ya nuna alhininsa kan rasuwar Danlami Abdullahi Saku
- Umaru Bago ya bayyana rasuwar a matsayin abin tausayi sannan ya miƙa saƙon ta'aziyyarsa ga iyalansa da al'ummar jihar Neja baki ɗaya
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Neja - Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago ya bayyana matuƙar alhininsa game da rasuwar shugaban ƙaramar hukumar Katcha, Danlami Abdullahi Saku.
Shugaban ƙaramar hukumar ta Katcha, ya rasa ransa ne a wani hatsarin mota da ya rutsa da shi kusa da Kwakuti a kan hanyar Minna zuwa Suleja.
Ta'aziyyar Gwamna Bago na cikin wata wata sanarwa ne da babban sakataren yada labaransa, Bologi Ibrahim ya fitar a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Bago ya yi ta'aziyya
Gwamna Umaru Bago ya bayyana rasuwar marigayin a matsayin abin ban tausayi, yana mai cewa hakan ya zama abin tunatarwa cewa, dukkan halittu daga Allah suke kuma za su koma gare shi idan lokacinsu ya yi.
Ya kuma yi addu’ar Allah Ya jiƙan marigayi Danlami Abdullahi Saku, sannan Ya sanya shi a cikin Aljannar Firdausi tare da bayar haƙurin jure wannan rashin ga iyalansa.
Gwamnan ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan mamacin, al’ummar ƙaramar hukumar Katcha, da ɗaukacin mutanen jihar baki ɗaya, bisa wannan babban rashin da aka yi.
Marigayin dai ya rasu ne bayan wani hatsarin mota ya ritsa da shi da misalin ƙarfe 7:00 na dare, a ranar Talata, 10 ga watan Disamban 2024.
Gwamna Bago zai raba kwamfutoci
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Neja ƙarƙashin jagorancin Gwamna Mohammed Umaru Bago, ta shirya farfado da fannin ilmi.
Gwmamnatin ta sanar da shirin rarraba kwamfutoci miliyan 1 ga makarantun gwamnati a faɗin jihar
Gwamna Umaru Bago ya bayyana hakan ne yayin wani taron shugabannin gargajiya da na addini a birnin Minna kan mahimmancin ilimin mata a shiyyar Arewa ta Tsakiya.
Asali: Legit.ng