Shekarau: Kotu Ta Mika Sammaci ga Tsohon Gwamnan Kano, An Ji Dalili

Shekarau: Kotu Ta Mika Sammaci ga Tsohon Gwamnan Kano, An Ji Dalili

  • Wata babbar kotun shari'ar musulunci da ke Kano, ta buƙaci tsohon gwamnan jihar, Sanata Ibrahim Shekarau ya bayyana a gabanta
  • Kotun ta miƙa sammaci ga tsohon gwamnan ne kan wata taƙaddama da ake yi na wani fili da ya ba makarantar Islamiyya
  • Iyayen yara da malaman makaranta ne dai suka shigar da ƙara a gaban kotun bayan waɗanda aka ba amanar filin sun sayar da shi

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Wata babbar kotun shari’ar Musulunci da ke Kano da ke zamanta a Shahuci ta miƙa sammaci ga Sanata Ibrahim Shekarau.

Kotun ta miƙa sammaci ga tsohon gwamnan na Kano ne kan wani fili da ake taƙaddama a kai, wanda ya ba wata makarantar Islamiyya da ke Layin Mai Unguwa, Sabuwar Gandu a ƙaramar Hukumar Kumbotso.

Kotu ta ba Shekarau sammaci
Kotu ta mika sammaci ga Sanata Ibrahim Shekarau Hoto: Mallam Ibrahim Shekarau
Source: Facebook

Malam Ibrahim Shekarau ya ba da kyautar fili

Kara karanta wannan

Abba ya ziyarci daliban Kano a kasar Indiya, zai cigaba da daukar nauyin karatun talakawa

Jaridar Daily Trust ta ce a shekarar 2021 ne tsohon gwamnan ya bayar da kyautar filin ga makarantar Imam Maliki bn Anas Litahfizul Qur’an Wattarbiyya Watta’alim a wajen bikin yaye ɗalibanta.

Sai dai ƴan uwan Ibrahim Shekarau da aka ba wa amanar filin ba su ji daɗin hakan ba, suka sayar da shi ga wani mutum.

Iyayen yara da malaman makarantar sun shigar da ƙara suna neman kotu ta mayar musu da filin da Shekarau ya bayar, a wasiƙar da ya sanyawa hannu a ranar 14 ga watan Agusta, 2021.

Sulhu bai yiwu ba kan rigimar filin Shekarau

Alƙalin kotun, Muhammad Sani Abdullahi, a zama na ƙarshe, ya gabatar da zaɓin sulhu amma waɗanda suke ƙara sun nuna ba su yarda ba.

Lauyan masu shigar da ƙara, Barista Hussain Muhammad Makari, ya buƙaci kotun da ta ba Shekarau sammaci da kuma sauran da aka ambato a cikin shari'ar amma ba su bayyana a gabanta ba.  

Muhammad Sani Abdullahi ya ɗage ci gaba da sauraron ƙarar har zuwa ranar 17 ga watan Disamba, domin ba da sammacin ga waɗanda ke cikin ƙarar.

Kara karanta wannan

Mummunar gobara ta laƙume kayan miliyoyin Naira a babban birnin jihar Kwara

Ibrahim Shekarau ya faɗi wani sirrinsa

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kano, Mallam Ibrahim Shekarau, ya fito ya bayyana wani sirrinsa da duniya ba ta san da shi ba.

Tsohon sanatan ya bayyana cewa lokacin da ya tsaya takarar gwamnan jihar Kano, yana da ƙasa da N100,000 a asusunsa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng