'Yan Kudu Sun Bi Sahun Masu Adawa da Kudirin Harajin Gwamnatin Tinubu
- Ƙungiyar matasan Niger Delta (NDYC) ta bi sahun masu nuna adawa da ƙudirin haraji na gwamnatin mai girma Bola Tinubu
- Matasan sun yi watsi da ƙudirin harajin wanda suka bayyana a matsayin wanda zai amfani wasu yankuna ƙalilan kawai
- Ƙungiyar 'yan kudancin Najeriyar ta buƙaci majalisar tarayya ta yi watsi da ƙudirin domin a cike yake da tarin kura-kurai
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Ƙungiyar matasan Neja-Delta (NDYC) ta yi watsi da ƙudirin sake fasalin haraji da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta gabatar.
Ƙungiyar NDYC ta bayyana ƙuɗirin a matsayin wanda ya kauce daga kan tsarin daidaito wanda aka gina al'ummar ƙasar nan a kansa.

Source: Facebook
Matasan sun bayyana hakan ne a ranar Talata, a wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun jagoran NDYC na ƙasa, Kwamared Israel Uwejeyan, cewar rahoton jaridar Tribune.
Ƙungiyar NDYC ta yi watsi da ƙudirin haraji
Ƙungiyar ta nuna cewa ƙudirin yana cike da kura-kurai, kuma zai ƙara tazara tsakanin ƴan kaɗan masu gata da kuma mafiya rinjaye da ke shan wahala, rahoton The Guardian ya tabbatar.
"Wannan ƙudirin wanda aka nuna shi a matsayin mafita ga ƙalubalen ɓangaren kuɗi a Najeriya, yana cike da kura-kurai waɗanda suka fifita wasu yankunan shafaffu da mai, yayin da ya bar wasu musamman yankin Neja Delta a baya."
"Dole ne mu tunatar da al’umma cewa, a zamanin dalar gyada, an yi amfani da arziƙin da aka samu daga albarkatun noma na Arewa, wajen gina muhimman ababen more rayuwa a Kudancin Najeriya."
"Amma duk da haka, a yau, an kawo wasu tsare-tsare da ke neman wargaza wannan al'ada ta samun ci gaba a tare, ta hanyar maida hankali wajen ba da fifiko ga wasu tsirarun jihohi masu masana'antu yayin da aka bar wasu a baya."
"Muna kira ga majalisar tarayya da ta yi watsi da wannan ƙudiri, a maimakon haka, ta kawo waɗanda za su amfani ƴan Najeriya baki ɗaya."
- Israel Uwejeyan
Ɗan majalisar Kano ya caccaki ƙudirin haraji
A wani labarin kuma, kun ji cewa wani ɗan majalisa daga jihar Kano ya caccaki ƙudirin haraji da gwamnatin Bola Tinubu ke son a amince da shi.
Ghali Mustapha ya bayyana cewa ƴan majalisa za su yi bakin ƙoƙarinsu domin ganin cewa ba a amince da ƙudirin ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng

