Tinubu Ya Fito Ya Fadi Matsalolin da Gwamnatinsa Ke Magancewa

Tinubu Ya Fito Ya Fadi Matsalolin da Gwamnatinsa Ke Magancewa

  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi magana kan matsalolin da gwamnatinsa ta gada daga wajen gwamnatocin baya
  • Bola Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa na ƙoƙarin magance matsalolin da ta gada daga wajen waɗanda suka gabace ta
  • Shugaban ƙasan ya nuna cewa yana sane da halin da ƴan Najeriya suke ciki sakamakon matakan da gwamntinsa ta ɗauka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Abia - Shugaba Bola Tinubu ya ce a hankali yana magance matsalolin tattalin arziƙi da gwamnatinsa ta gada.

Shugaba Tinubu ya kuma yarda da matsalolin da ƴan Najeriya ke ciki, sakamakon matakan da gwamnatinsa ta ɗauka.

Tinubu ya yi magana kan matsalolin da ya gada
Tinubu yace yana magance matsalolin da ya gada Hoto: @DOlusegun
Asali: Facebook

Tinubu ya bayyana haka ne a jiya Asabar, jawabin da ya gabatar a wajen bikin yaye ɗalibai karo na 12, na jami’ar noma ta Micheal Okpara da ke Umudike (MOUAU), jihar Abia, cewar rahoton jaridar Leadership.

Kara karanta wannan

"'Yan siyasa na shan wuya": Shugaban majalisa ya mika kokensa gaban gwamna

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me Tinubu ya ce kan matsalolin Najeriya

Shugaba Tinubu ya samu wakilcin darakta a ma’aikatar noma da samar da abinci, Dokta Deola-Tayo Lordbanjou, a wajen taron.

Shugaban ƙasan bayyana cewa gwamnatinsa ta karɓi ƙalubalen tunkarar matsalolinmu.

"Babu hanyoyi masu sauƙi wajen magance waɗannan matsalolin, amma ba na tantamar cewa mutanenmu za su yi farin ciki idan aka aiwatar da matakan domin shawo kan matsalolin."

- Bola Tinubu

Shugaban ya ƙara da cewa, ya taya ɗaliban, iyayensu, masu kula da su, abokansu, da masu fatan alheri, murna saboda nasarorin da suka samu.

Karanta wasu labaran kan Tinubu

Uba Sani ya gana da Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya gana da Shugaban Bola Ahmed Tinubu a fadar shugaban kasa (Aso Rock) da ke Abuja.

A yayin taron, Uba Sani ya gabatarwa Tinubu rahoto kan kokarin da ake ci gaba da yi domin magance matsalolin tsaro da cigaban jihar Kaduna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng