Wasu Shugabannin Ƴan Bindiga da Ake Nema Sun Miƙa Wuya ga Sojoji, DHQ Ta Jero Sunaye

Wasu Shugabannin Ƴan Bindiga da Ake Nema Sun Miƙa Wuya ga Sojoji, DHQ Ta Jero Sunaye

  • Hedkwatar rundunar soji ta ƙasa (DHQ) ta ce wasu manyan jagororin ƴan ta'adda sun miƙa wuya ga sojoji a makon da ya gabata
  • Kakakin DHQ, Manjo Janar Edward Buba ya jero sunayen wasu daga ciki, ya ce akwai waɗanda suka nuna sha'awar ajiye makamai
  • Buba ya kara da cewa a tsawon makon da ya wuce, sojoji sun kashe ƴan ta'adda 135, sun ceto nutane 129 da aka yi garkuwa da su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Hedkwatar rundunar sojin Najeriya (DHQ) ta bayyana cewa manyan jagororin ƴan ta'adda da take nema ruwa a jallo sun mika wuya ga sojoji.

Shugabannin ƴan ta'addan da suka tuba suka miƙa wuya sun haɗa da Yellow Jambros, Alhaji Mallam, Ardo Idi (Alhaji Lawal), Lawal Kwalba, Salkado, Yellow Ibrahim, Gana’e Babangida da sauransu.

Kara karanta wannan

"Ku ceto mijina:" Uwargidan kusa a APC ta nemi dauki kwanaki bayan 'sace' shi

CDS Musa.
Hedkwatar tsaro ta ce jagororin ƴan ta'adda sun miƙa wuya ga sojoji a Najeriya Hoto: @DefenceInfoNG
Asali: Facebook

Daraktan yaɗa labarai na DHQ, Manjo Janar Edward Buba ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar yau Juma'a a Abuja, Leadership ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Wasu shugabannin ƴan bindiga sun tuba" - Sojoji

Buba ya ce waɗannan manyan hatsabiban ƴan ta'addan waɗanda ke cikin jerin da ake nema ruwa a jallo, sun miƙa wuya ga sojoji ne a mako guda da ya gabata.

Kakakin DHQ ya ƙara da cewa bayan waɗannan, akwai wasu ƙasurguman ƴan ta'addan da suka nuna sha'awar ajiye makamai su rungumi zaman lafiya.

Manjo Janar Buba ya kuma bayyana cewa sojoji sun kashe ‘yan ta’adda 135, sun kama wasu 185 tare da kubutar da mutane 129 da aka yi garkuwa da su a cikin makon jiya.

Sojojin Najeriya sun matsawa ƴan ta'adda

Mai magana da yawun hedikwatar ya ce manyan ‘yan ta’addan sun miƙa wuya ne sakamakon luguden wutar da sojoji suka yi masu a makonnin baya-bayan nan.

Kara karanta wannan

Mutumin Gombe da ya niƙi gari ya tafi Abuja a keke ya samu kyautar mota da kudi

"Ya zuwa yanzu da dama daga cikin shugabannin ‘yan ta’adda, kwamandoji da mayaka sun mika wuya, wasu ma sun nuna sha’awar mika wuya," in ji shi.

Sojoji sun kama infoma a Taraba

Kun ji cewa sojoji sun damke wani mutumi ɗan shekara 73, Alhaji Buba Maru, bisa zargin taimakawa ƴan bindiga da bayanai a jihar Taraba.

Dakarun rundunar sojoji ta cafke mutumin ne a lokacin da suka fita kai samamen tsaftace wasu yankuna daga ayyukan ƴan bindiga.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262