Gwamna Umo Eno Ya Ayyana Ranar Hutu a Jiharsa, Ya Bayyana Dalili
- Gwamnatin jihar Akwa Ibom na ci gaba da shirye-shiryen birne uwargidan Mai girma Gwamna Umo Eno da ta rasu
- A cigaban da shirye-shiryen sada marigayiyar da makwancinta, gwamnatin ta ayyana ranar Juma'a a matsayin ranar hutu
- Gwamnatin ta ce ta ba da hutun ne domin ba mutanen jihar damar karrama marigayiyar tare da yi mata bankwana
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Akwa Ibom - Gwamnatin Akwa Ibom ƙarƙashin jagorancin, Gwamna Umo Eno, ta ayyana ranar Juma’a, 29 ga watan Nuwamba a matsayin ranar da babu aiki a jihar.
Gwamnatin ta ba da hutun ne domin karrama uwargidan gwamnan jihar, marigayiya Fasto Patience Umo Eno.
Sakataren gwamnatin jihar, Prince Enobong Uwah, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa mai ɗauke da kwanan watan ranar Laraba, 27 ga watan Nuwamba, cewar rahoton jaridar The Sun.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Meyasa aka ba da hutu a Akwa Ibom?
Prince Enobong Uwah ya bayyana cewa an ba da hutun ne a shirye-shiryen da ake yi na kai marigayiyar zuwa makwancinta, rahoton The Punch ya tabbatar.
Ya ƙara da cewa an ba da hutun ne bayan an tuntuɓi iyalan marigayiyar.
Gwamnatin jihar ta sanar da rasuwar uwargidan gwamnan bayan ƴar gajeriyar jinya da ta yi a wani asibiti, a ranar 26 ga watan Satumban 2024.
"A shirye-shiryen birne marigayiya, Fasto Patience Umo Eno, gwamnatin jihar Akwa Ibom ta hanyar tuntuɓar iyalan mai rasuwar, ta ayyana ranar Juma'a, 29 ga watan Nuwamba a matsayin ranar da babu aiki domin karrama ta."
"An yi hakan ne domin ba ƴan jihar Akwa Ibom damar yi mata bankwana a inda za a ajiye ta a wannan ranar a Ikot Ekpene Udo, ƙaramar hukumar Nsit Ubium."
- Prince Enobong Uwah
Gwamna Uno ya magantu kan mutuwar matarsa
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Akwa Ibom, Umo Eno ya yi magana sa'o'i kaɗan bayan sanar da mutuwar matarsa da safiyar ranar Jumu'a, 27 ga watan Satumba, 2024.
Gwamna Eno ya godewa masu ta'aziyya da fatan alheri ga iyalansa, inda ya tabbatar da cewa lamarin ba zai shafi harkokin tafiyar da gwamnatinsa ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng