Jirage 2 Sun Gamu da Mummunan Hatsari Ana cikin Tsala Gudu, An Rasa Rayuka

Jirage 2 Sun Gamu da Mummunan Hatsari Ana cikin Tsala Gudu, An Rasa Rayuka

  • Wasu jiragen ruwa biyu sun yi karo a yankin ƙaramar hukumar Warri ta Kudu a jihar Delta, mutum biyar sun rasa rayukansu
  • Rundunar ƴan sanda ta tabbatar da faruwar lamarin, ta ce wasu sun samu raunuka kuma an kwantar da su a asibiti domin yi masu magani
  • An ruwaito cewa har yanzun ba a ga sauran fasinjoji 20 da hatsarin ya rutsa da su ba amma jami'an ba da agaji na ci gaba da lalube a ruwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Delta - Akalla mutum biyar sun rasa rayukansu sakamakon wani mummunan hatsarin jiragen ruwa da ya afku a yankin ƙaramar hukumar Warri ta Kudu a jihar Delta.

Wasu mutum shida sun samu raunuka a hatsarin yayin da wasu mutane 20 kuma suka ɓata har yanzu ba a gansu ba.

Kara karanta wannan

An kama yan ta'adda da miyagu 523, an ceto mutane 102 a Kaduna

Taswirar jihar Delta.
Hatsarin Jirgi ya yi ajalin mutum 5, wasu da dama sun bata a Delta Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Ƴan sanda sun tabbatar da hatsarin jirage 2

Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan jihar Delta, Edafe Bright ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai, Channels tv ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce tuni aka garzaya da waɗanda suka samu raunuka wani asibiti domin a yi masu magani.

Hatsarin dai ya rutsa da wasu jiragen ruwa guda biyu ne a lokacin da suka ɗauko wau ƴan gida ɗaya da suka dawo daga wurin bikin jana'iza.

Yadda jiragen ruwa suka yi hatsari

An tattaro cewa jiragen ruwan, waɗanda ke tsula gudu sun yi taho mu gama, lamarin da ya yi ajalin mutum biyar daga cikin fasinjoji.

Gaba ɗaya fasinjojin suka nutse a ruwa bayan jiragen sun yi karo kuma dukkansu babu mai sanye da rigar ruwa.

A halin yanzu dai jami'an bada agaji da sauran mutanen yanki na ci gaba da laluben waɗanda suka nutse da nufin gano ko da gawarwakinsu ne, Tribune ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Abia: Dakarun sojoji sun far wa ƴan Bindiga, an fara musayar wuta mai zafi

Najeriya na fama da yawan haɗurran jiragen ruwa wanda ke jawo asarar rayukan bayin Allah a jihohi da dama.

Jirgin ruwa ya yi hatsari a Zamfara

A wani rahoton, kun ji cewa wani hatsarin jirgin ruwa da ya auku a jihar Zamfara ya yi sanadiyyar rasuwar mutane masu tarin yawa.

Rahotanni sun bayyana cewa aƙalla mutane sama da 40 ne suka rasu sakamakon hatsarin wanda ya auku a ƙaramar hukumar Gummi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262