Hukumar Hisbah Ta Waiwayo kan Masu Shagunan Caca a Kano
- Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta gamsu da hukuncin da Kotun Ƙoli ta yanke kan taƙaddamar dokar caca
- Daraktan Hisbah a Kano ya bayyana cewa za su ci gaba da kai samame kan shagunan da ake yin caca a jihar
- Aliyu Sufi ya ƙara da cewa dama tuntuni suna adawa da dokar caca wacce a shari'ance ta ba da goyon baya ga yin caca
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Hukumar Hisbah a jihar Kano ta yi magana kan matsalar samun shagunan caca a jihar.
Hukumar Hisbah ta bayyana cewa za ta ci gaba da kai samame kan shagunan bayan hukuncin da Kotun Ƙoli ta yanke kan dokar caca.
Darakta a hukumar Hisbah ta jihar Kano, Aliyu Sufi, ya bayyana hakan, cewar rahoton tashar Channels tv.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kotu ta soke dokar cacca
A ranar Juma'a Kotun Ƙoli ta soke wata dokar shekarar 2005 wacce ta kafa hukumar yin caca ta ƙasa tare da halatta yin caca.
Kotun ta yanke hukuncin cewa kula da harkokin caca lamari ne na gwamnatocin jihohi.
Hisbah za ta dura kan shagunan caca a Kano
Daraktan na Hisbah ya bayyana cewa yanzu da kotu ta yanke wannan hukuncin, za su ci gaba da kai samame kan shagunan caca, rahoton Tribune ya tabbatar.
"Za mu dawo da murƙushe shagunan caca cike da jajircewa tunda yin caca ya saɓawa doka a ƙarƙashin dokar shari'ar musulunci ta Kano."
"Da wannan hukuncin, an kawo ƙarshen taƙaddamar da ake kan wanda ya kamata ya kula da dokar caca tsakanin gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi."
"Mu a Kano muna adawa da dokar caca, saboda ta ba da goyon baya a shari’ance ga caca wacce Musulunci ya haramta."
- Aliyu Sufi
Hisbah ta lalata barasa a Yobe
A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar Hisbah ta jihar Yobe ta lalata kwalaben barasa sama da 170 waɗanda kuɗinsu ya kai N450,000.
An ƙwace kwalaben ne a ɗaya daga cikin otal ɗin da ke garin Gashua, hedkwatar ƙaramar hukumar Bade.
Asali: Legit.ng