Yan Bindiga Sun Sace Ƴan Uwan Ɗan Jarida Ana Tsaka da Jimamin Rasuwar Mahaifiyarsa

Yan Bindiga Sun Sace Ƴan Uwan Ɗan Jarida Ana Tsaka da Jimamin Rasuwar Mahaifiyarsa

  • Ƴan bindiga sun sace ƴan uwan wani ɗan jarida, Ahmed Ajobe kwanaki kaɗan bayan rasuwar mahaifiyarsa a jihar Kogi
  • An ruwaito cewa maharan sun nemi a biya su Naira miliyan 50 a matsayin kuɗin fansar mutum uku da suka sace ranar Alhamis
  • Rundunar ƴan sandan jihar Kogi ta bayyana cewa ta tura dakaru zuwa yankin domin ceto waɗanda aka sace cikin ƙoshin lafiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kogi - Ƴan bindiga sun yi garkuwa da ƴan uwan tsohon editan jaridar Daily Trust, Malam Ahmed Ajobe a jihar Kogi da ke Arewa ta Tsakiya.

Wadanda abin ya shafa sun hada da namiji daya da mata biyu, ciki har da kanwar Ahmed Ajobe mai suna Halimtu-Sadiya Tahir.

Taswirar jihar Kogi.
Yan bindiga sun yi garkuwa da ƴan uwan wani ɗan jarida a jihar Kogi Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Channels tv ta ruwaito cewa ƴan bindigar sun sace su ne a kan hanyarsu ta zuwa wata kasuwa da ke kusa da garin Awo, karamar hukumar Ankpa ta jihar Kogi.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun hallaka manoma 7, sun ƙona buhunan masara 50 a jihar Neja

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A ranar Lahadin da ta gabata, mahaifuyar ɗan jaridar, Malama Aishetu Tahir ta rasu bayan fama da doguwar jinya.

Ƴan bindiga sun sace ƴan uwan ɗan jarida

An tattaro cewa yana shirye-shiryen gudanar da addu'ar bakwai ne kuma ƴan uwansa suka faɗa hannun masu garkuwa da mutane.

Haka nan kuma bayanai sun nuna cewa ƴan uwan ɗan jaridar sun baro gida ne da nufin zuwa kasuwa sayo kayan addu'ar bakwai suka ci karo da ƴan bindiga.

Masu garkuwa sun nemi kudin fansa

Duk da ba a samu jin ta bakin Ahmed Ajobe ba, wani abokinsa ya ce masu garkuwa sun kira sun nemi Naira miliyan 50 a matsayin kuɗin fansa.

“Masu garkuwa sun kira waya a ranar Juma’a da yamma inda suka bukaci a biya su Naira miliyan 50 a matsayin kudin fansa. Ban da tabbacin ko an fara tattaunawa saboda na yi tafiya."

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun yi garkuwa da basarake da wasu mutane 14 a jihar Kaduna

"Abin da nake da tabbatas shi ne har yanzu ba a kai masu kuɗi ba kuma waɗanda aka sace suna can a hannunsu," in ji shi.

Wane mataki ƴan sanda suka ɗauka?

Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kogi, (PPRO), William Aya, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce tuni DPO mai kula da yankin ya tura dakarun ƴan sanda domin tabbatar da ceto wadanda aka yi garkuwa da su, Punch ta ruwaito.

Kaduna: An yi garkuwa da basarake

A wani labarin, kun ji cewa ƴan bindiga sun kai farmaki kauyen Ungwan Babangida da ke ƙaramar hukumar Kauru a jihar Kaduna, sun sace mutane 15.

Wani shugaban matasa, Aminu Khalid ya ce Magajin garin na cikin waɗanda maharan suka yi garkuwa da su ranar Alhamis da daddare.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262