Bola Tinubu Ya Buƙaci Majalisar Dattawa Ta Amince da Naɗin Sabon Hafsan Sojojin Kasa
- Shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya bukaci majalisar dattawa ta amince da naɗin Laftanar Janar Oluyede a matsayin hafsan sojin kasa
- Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma'a
- A watan Oktoba Tinubu ya nada Oluyede a matsayin mukaddashin hafsan sojin ƙasa sakamakon rashin lafiyar Taoreed Lagbaja
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya bukaci majalisar dattawa ta amince da Laftanar Janar Olufemi Oluyede a matsayin hafsan sojojin kasa (COAS).
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da kakakin shugaban kasa, Bayo Onanuga ya fitar ranar Juma'a, 22 ga wstan Nuwamba, 2024.

Asali: Twitter
Onanuga ya ce matakin na Tinubu ya yi daidai da tanadin kundin tsarin mulkin Najeriya, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tinubu ya bukaci tabbatar da naɗin COAS
Ya ce shugaban ƙasa ya tura wasika a hukumance zuwa majalisar dattawa domin tantancewa da tabbatar da sabon hafsan rundunar sojojin ƙasa.
"Shugaba Bola Tinubu ya aika wasika ga majalisar dattawa yana neman a tabbatar da Laftanar Janar Olufemi Olatubosun Oluyede a matsayin babban hafsan sojin ƙasa (COAS).
“A wasikar da ya aika a yau, Tinubu ya nemi tabbatar da naɗin Oluyede bisa tanadin sashe na 218 (2) na kundin tsarin mulkin 1999 da kuma sashe na 18 (1) na dokar sojoji."
Yadda Tinubu ya naɗa muƙaddashin COAS
An nada Oluyede a matsayin mukaddashin babban hafsan sojojin ƙasa a ranar 30 ga watan Oktoba sakamakon rashin lafiyar Laftanar Janar Taoreed Lagbaja.
Amma daga bisani, Janar Lagbaja ya rasu a ranar 5 ga watan Nuwamba, 2024 kuma tuni aka birne shi a birnin tarayya Abuja.
A yanzu kuma Shugaba Tinubu ya bukaci majalisa ta amince da naɗinsa a matsayin COAS.
Ya ce yana da kwarin guiwar cewa zai iya jan ragamar sojojin ƙasa wajen tabbatar da zaman lafiya a ƙasar nan, kamar yadda The Nation ta kawo.
Tinubu ya karrama marigayi Lagbaja
Kuna da labarin cewa Bola Ahmed Tinubu ya karrama marigayi shugaban rundunar sojojin ƙasa, Taoreed Lagbaja da lambar yabo ta kasa CFR.
Shugaban ƙasar ya ce Lagbaja na ɗaya daga cikin mutanen da yake alfahari .da naɗinsu bayan hawansa kan madafun iko.
Asali: Legit.ng