Gwamma Ya Kere N70,000, Ya Faɗi Sabon Albashin da Zai Fara Biyan Ma'aikata

Gwamma Ya Kere N70,000, Ya Faɗi Sabon Albashin da Zai Fara Biyan Ma'aikata

  • Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke ya sanar da sabon mafi karancin albashin da zai fara biyan ma'aikatan gwamnati
  • A wata sanarwa, kwamishinan yaɗa labaran Osun ya ce Gwaman Adeleke ya amince da N75,000 a matsayin sabon albashi mafi kanƙanta
  • Gwamna Adeleke ya bukaci ma'aikata su kara kaimi wajen sauke nauyin da ke kansu tare da lalubo sababbin hanyoyin kawo ci gaba a Osun

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Osun - Gwamna Ademola Adeleke na Osun ya amince da N75,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashin ma'aikatan gwamnati a jihar.

Gwamnan ya amince da sabon ƙaramin albashin ne bayan zaman tattaunasa da ƙungiyoyin ƴan kwadago na jihar Osun.

Gwamna Ademola Adeleke.
Gwamnan Osun, Ademola Adeleke ya amince da N75,000 a matsayin sabon mafi karancin albashi Hoto: @Osun_State_Gov
Asali: Twitter

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da gwamnatin jihar Osun ta wallafa a shafinta na manhajar X da safiyar yau Laraba, 20 ga watan Nuwamba, 2024.

Kara karanta wannan

Zanga zanga ta ɓarke kan harbin hadimin gwamna a ofishin ƴan sanda, bayanai sun fito

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Adelele ya haura N70,000

Da yake ƙarin haske kan lamarin, kwamishinan yaɗa labarai, Oluomo Kolapo Alimi ya ce Gwamna Adeleke ya ɗauki ma'aikata da matuƙar muhimmanci.

A cewarsa, gwamna ya amince da N75,000 wanda ya kere dokar sabon albashi ta N70,000 bayan karɓar rahoton kwamitin da ya kafa don tattaunawa da ƴan kwadago.

Kwamishinan ya ce tawagar gwamnati karkashin jagorancin shugaban ma'aikatan gwamna, Kazeem Akinleye ta zauna da ƴan kwadago har aka cimma matsaya.

Gwamna ya roki ma'aikata su ƙara ƙaimi

Wani sashin sanarwar ya ce:

"Gwamnatin Ademola Adeleke ta himmatu wajen inganta walwala da jin daɗin ma'aikata waɗanda ssuka jajirce suna aiki tukuru ba tare da gajiyawa ba."

Gwamnan Adeleke, a cewar Oluomo Alimi, ya bukaci ma’aikatan jihar da su kara kaimi wajen gudanar da ayyukansu domin sauke nauyin da ya rataya a kansu.

Ya kuma roki ma'aikatan su lalubo sababbin hanyoyin warware matsalolin da za su inganta aikin gwamnati tare da tabbatar da gaskiya da rikon amana.

Kara karanta wannan

Gwamna ya samu ƙarin dama daga Majalisa, zai naɗa sababbin hadimai 20

Gwamnan Ekiti ya amince da N70,000

Kun ji cewa Gwamna Biodun Oyebanji ya amince da N70,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi ga ma'aikatan gwamnati a jihar Ekiti.

A wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, Mai girma Gwamna Oyebanji ya ce ƙarin albashin zai shafi har ƴan fansho da ke jihar

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262