APC Ta Tura Ƴan daba Sun Hargitsa Zaben Gwamnan Jihar Ondo? Jam'iyya ta magantu
- Jam’iyyar APC ta musanta zargin PDP na aika da ‘yan daba zuwa Ofosun domin hargitsa zaben gwamnan Ondo da ake gudanarwa
- Kakakin jam'iyyar APC a Ondo, Steve Otaloro ya ce ana gudanar da zabe cikin lumana, kuma babu hannunta a tayar da tarzoma
- Otaloro ya kara da cewa APC ta jajirce wajen tabbatar da anyi zaben cikin luma inda ya nemi sauran jam'iyyun siyasa su bi doka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Ondo - Jam'iyyar APC ta yi martani yayin da aka zargeta da tura 'yan daba zuwa karamar hukumar Idanre domin hargitsa zaben gwamnan Ondo.
Sakataren watsa labaran APC na jihar Ondo, Steve Otaloro ya ce zargin da jam'iyyar PDP ke yi na cewar sun tura 'yan daba garin Ofosun ba gaskiya ba ne.
Ondo: APC ta karyata zargin PDP
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa kakakin jam'iyyar ya ce bayanan da suka samu sun nuna cewa "babu wani abu makamancin haka."
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yayin da yake magana daga dakin sa ido na APC, Otaloro ya ce, babu kamshin gaskiya a zarginda mataimakin dan takarar PDP ya yi.
Steve Otaloro ya tuna cewa PDP ta gudanar da taron manema labarai kwanaki biyu baya, inda ta zargi APC da haddasa tashin hankalula a Idanre ba tare da bayar da hujjoji ba.
Otaloro ya kalubalanci mataimakin dan takarar PDP da ziyartar wuraren da ake zargin an kaiwa harin, inda ya bashi shawarar tsayawa a rumfar zabensa.
Ondo: APC ta aika sako ga jam'iyyu
Ya kara da cewa:
“Ana ci gaba da kada kuri’a cikin lumana. Idan akwai wata matsala, ya kamata a bincike ta yadda ya dace, amma zan tabbatar muku ba daga jam'iyyar ba ne.”
Ya musanta zargin cewa 'yan APC sun kai hari a garuruwan da ke nesa da birane yana mai bayyana irin wannan zargin da makircin siyasa.
Otaloro ya jaddada jajircewar APC wajen tabbatar da zaman lafiya a zaben, yana kira ga dukkan jam’iyyun da su rungumi zaman lafiya yayin zaben.
Asali: Legit.ng