Shugaba Tinubu Ya Shiga Ganawa da Ministoci da Manyan Ƙusoshin Gwamnati a Abuja

Shugaba Tinubu Ya Shiga Ganawa da Ministoci da Manyan Ƙusoshin Gwamnati a Abuja

  • Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya jagoranci taron majalisar zartaswa (FEC) a fadar gwamnati da ke Abuja yau Alhamis, 14 ga watan Nuwamba
  • Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima, shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila da ministoci sun halarci taron
  • Duk da babu wata sanarwa a hukumance amma ana hasashen taron zai maida hankali ne kan shirye-shiryen kasafin kudin 2025

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya shiga taron majalisar zartaswa ta ƙasa watau FEC yanzu haka a Aso Villa da ke birnin tarayya Abuja.

Wannan taron na zuwa ne mako guda bayan Shugaba Tinubu ya soke taron FEC da aka shirya yi ranar Laraba a makon jiya.

Taron FEC.
Bola Tinubu ya shiga taron FEC a fadar shugaban kasa Hoto: @aonanuga1956
Asali: Twitter

Dalilin Shugaba Tinubu na ɗage taron FEC

Bola Tinubu ya ɗage taron ne sakamakon mutuwar hafsan rundunar sojojin ƙasa ta Najeriya (COAS), Laftanar Janar Taoreed Lagbaja, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Abin da Yariman Saudiyya ya faɗawa Bola Tinubu kan cire tallafin mai da wasu tsare tsare

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An tattaro cewa an fara taron FEC na yau Alhamis, 13 ga watan Nuwamba, 2024 da misalin karfe 1:11 na rana karkashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu.

Manyan kusoshin gwamnati sun halarta

Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima da shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila sun halarci taron na yau Alhamis.

Sauran waɗanda aka hanga sun shiga zaman FEC sune shugaban ma'aikatan gwamnatin tarayya, Mrs Didi Walson-Jack da wakilan sakataren gwamnati (SGF).

Rahoton Daily Trust ya nuna cewa kusan dukkan ministoci da sauran ƴan majalisar zartaswa sun halarci taron a wannan mako.

Ana hasashen dai taron FEC na yau na da alaƙa da shirye-shiryen kasafin kuɗin 2025 wanda majalisar tarayya ke dakon Shugaba Tinubu ya gabatar.

Shugaba Tinubu ya yi naɗe-naɗe a INEC

A wani rahoton, an ji cewa Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya naɗa ƙarin kwamishinoni biyu a hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa watau INEC.

Bola Tinubu ya naɗa Abdulrazak Yusuf Tukur a matsayin kwamishinan INEC da zai kula da shiyyar Arewa maso Yamma a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262